Shugaba Tinubu Ya Kara Wa Ma’aikatan Gwamnati Albashi Na Wucin Gadi

Shugaba Tinubu Ya Kara Wa Ma’aikatan Gwamnati Albashi Na Wucin Gadi

  • Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya bayyana karin albashi ga wasu bangare na ma'aikata a Najeriya
  • Ya bayyana hakan ne yayin yiwa 'yan kasa jawabin murnar samun 'yancin kasa da sanyin safiyar yau
  • Sai dai, ta yaya wadanda ba ma'aikata ba za su samu ragin radadi a irin wannan yanayi duba da yanayin kasar nan?

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnatinsa ta dukufa wajen rage radadin da suke fuskanta sakamakon cire tallafin man fetur.

Ya yi hakan ne ta hanyar bayyana cewa, nan da watanni shida masu zuwa, matsakaitan ma’aikata za su rika samun karin Naira 25,000 duk wata a kan albashinsu.

A wani jawabi da aka watsa a gidan talabijin kasa a ranar murnar 'yanci, an shugaban yana bayyana shirinsa na karin albashin na wucin gadi.

Kara karanta wannan

An samu sauki: Tinubu zai ware talakawa miliyan 15 ya raba musu kudi, ya fadi yaushe

Tinubu ya karawa ma'aikata albashi
Shugaban kasa ya karawa ma'aikata albashi | Hoto: Asiwaju Bola Ahmad Tinubu
Asali: Facebook

Muna sauye-sauye a gwamnatinmu

A cewarsa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Mun fara sauye-sauye da dama a bangarorin gwamnati domin daidaita tattalin arzikin kasa, da manufofin kasafi da na kudi kai tsaye don yakar da hauhawar farashin kayayyaki."

Hakazalika, ya ce gwamnatin anasa za ta yi kokari wajen tabbatar da an samu karuwa ainun wajen samar da kayayyakin cikin guda don dogaro da kai.

A cewarsa, gwamnatin za ta "karfafa samar da kayayyakin cikin gida, tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi da bada rance da karin tallafi ga talakawa da marasa galihu.”

Ya yi karin albashi ga ma'aikata

Ya ce bisa tattaunawar da gwamnatinsa ta yi da ma’aikata, ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki, gwamnatin ta bullo da hanyar rage radadin ma'aikata.

Legit Hausa ta ji shugaban kasar na cewa:

"Nan da watanni shida masu zuwa, matsakaitan ma’aikata za su rika karbar karin Naira 25,000 a kowane wata a albashinsu."

Kara karanta wannan

Dole za ku sha wahala: Tinubu ya ce 'yan Najeriya su shirya shan kebura, gyara babu dadi

Sai dai, wadanda ba ma'aikata ba za su iya fuskantar matsaloli, domin tallafin da gwamnati ta bayar a raba a jihohi bai isa hannun da yawan talakawa ba.

Zan zage damtse wajen gyara kasa, inji Tinubu

Tinubu ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnatinsa na kara zage damtse wajen kawo matakan da za su kawar da mawuyacin halin da 'yan kasar ke ciki sakamakon cire tallafin man fetur da lalacewar darajar Naira.

Tinubu ya ba da wannan tabbacin ne a lokacin da yake jawabi a bikin faretin yaye sojiji da aka gidanar Kwalejin Tsaro ta Najeriya da ke Kaduna, The Nation ta ruwaito.

Shugaban wanda ya samu wakilcin mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ya ce hakazalika zai yi aiki wajen tabbatar magance talauci da ayyukan ta’addanci a dukkan kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.