Ana Tsaka da Jiran Bayani Daga Shugaban Kasa, Tinubu Zai Yiwa ’Yan Kasa Jawabi Gobe Lahadi

Ana Tsaka da Jiran Bayani Daga Shugaban Kasa, Tinubu Zai Yiwa ’Yan Kasa Jawabi Gobe Lahadi

  • Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu zai yiwa 'yan Najeriya jawabi a ranar murnar samun 'yan kai da za a yi
  • An ce Tinubu zai yi jawabin ne da misalin karfe 7 na safe a gobe Lahadi 1 ga watan Oktoba idan Allah ya kaimu
  • Shugaba Tinubu ya shafe kwanaki a kasar waje, 'yan Najeriya na ci gaba da sauraran abin da shugaban zai fada a makon nan

FCT, Abuja - Rahoton da ke fitowa daga fadar shugaban kasa ya bayyana cewa, shugaba Bola Ahmed Tinubu zai fitowa ya yiwa 'yan Najeriya jawabi, TheCable ta ruwaito.

Zai yi jawabi ga 'yan kasar nan ne a ranar Lahadi 1 ga watan Oktoba a daidai lokacin fara bikin murnar cika shekaru 63 da samun 'yancin Najeriya.

Kara karanta wannan

Saura kiris: Tinubu ya ce a kara hakuri, yana kan hada yadda zai ragewa 'yan kasa shan wahala

Wannan na fitowa ne daga wata sanarwar da mai ba Tinubu shawari kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale a ranar Asabar.

Shugaba Tinubu zai yiwa 'yan Najeriya jawabi
Shugaba Tinubu zai yiwa 'yan kasa jawabi | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Yaushe Tinubu zai yiwa 'yan kasa jawabi?

A cewarsa, Tinubu zai yiwa 'yan kasar jawabi ne da sanyin safiya da misalin karfe 7 na safe, rahoton Channels Tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce:

"Ana bukatar gidajen talabijin, radio da sauran kafafen yada labarai na zamani da su tsaya kyam ga gidan talabijin na kasa NTA da kuma gidan rediyon Najeriya don sauraran abin da za a fada."

Shugaba Tinubu dai bai jima da dawowa Najeriya ba, inda ya shafe kwanaki da yawa a kasar waje, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

'Yan Najeriya na ci gaba da jiran tsammani da bayanan shugaban kasa kan abin da zai biyo baya yayin da kungiyoyin kwadago ke shirin shuga yajin aiki a kasar.

Kara karanta wannan

Ku yi hakuri: NLC da TUC sun girgiza Najeriya, sanata ya roki su janye shirin yajin aiki

A yi hakuri da yajin aiki, sanata ga NLC

A wani labarin, yayin da Najeriya ke shirin bikin cika shekaru 63 da samun ‘yancin kai, shugaba a majalisar dattawa, Opeyemi Bamidele, ya roki kungiyar kwadago ta Najeriya da ta dakatar da shirin shiga yajin aikin sai baba-ta-gani.

Bamidele ya yi nuni da cewa, gwamnatin tarayya da dukkan hukumomin da abin ya shafa suna aiki domin samar da hanyoyin da suka dace wajen magance bukatun kungiyoyin kwadago.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, Bamidele ya taya 'yan Najeriya murnar cika shekaru 63 da samun 'yancin kai, rahoton Punch.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.