Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Mutane Sama da 30 a Jihar Neja

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Mutane Sama da 30 a Jihar Neja

  • Miyagun 'yan bindiga sun sake kai hari garuruwa biyu a yankin ƙaramar hukumar Munya da ke jihar Neja
  • Rahotanni sun bayyana cewa 'yan ta'addan sun yi garkuwa da mutane 31 ciki harda mata a harin na ranar Alhamis
  • Sanatan Neja ta Gabas, Sani Musa, ya koka kan yadda 'yan ta'adda ke ƙara matsa wa mutanen mazaɓarsa

Jihar Niger - Rahoton The Nation ya nuna cewa aƙalla mutane 31 daga ƙauyukan Kabula da Zagzaga a ƙaramar hukumar Munya ta jihar Neja suka faɗa hannun 'yan ta'adda.

Yan bindigan sun yi garkuwa da mutanen ne yayin da suka kai farmaki ƙauyukan biyu ranar Alhamis, 28 ga watan Satumba, 2023.

Harin 'yan bindiga a jihar Neja.
Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Mutane Sama da 30 a Jihar Neja Hoto: thenationonline
Asali: Twitter

Maharan sun yi awon gaba da mutane 23 daga ƙauyen Tsohon Ƙabula yayin da suka kwashi mata Takwas a garin Zagzaga duk a jihar Neja da ke Arewa ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Ta'adda Sun Sake Kai Ƙazamin Hari Jihar Kaduna, Sun Halaka Mutane da Yawa

Wannan farmakin na zuwa ne makonni biyu bayan 'yan ta'adda sun tarwatsa baki ɗaya ƙauyen Zagzaga, inda suka maida gidaje da shagunan jama'a tamkar mafakar su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda yan bindigan suka aikata wannan ɗanyen aiki

An tattaro cewa lokacin da adadi mai yawa na 'yan bindiga suka shiga ƙauyen, Mazajen garin suka ari na kare suka gudu, suka bar mata da ƙananan yara a gida.

Wannan ne ya bai wa 'yan ta'addan cikakkiyar damar sace mata takwasa ba tare da fuskantar tirjiya ba.

Wata majiya daga garin ta bayyana cewa:

"Wannan karon a ƙafa suka zo, amma sun zo da mayaƙa da yawa, ba zamu iya gane yawan su ba saboda duhu ya yi lokacin ƙarfe 7:00 na dare."
"Baki ɗaya mazan garin suka gudu zuwa cikin daji domin tsira da rayuwarsu amma duk da haka sai da suka tafi da mata guda takwas."

Kara karanta wannan

Yadda Yan Bindiga Suka Yi Awon Gaba Da Mata Da Yayanta a Wani Sabon Hari a Arewacin Najeriya

Sanata Musa ya yi magana kan halin da ake ciki

Sanata mai wakiltan Neja ta Gabas, Alhaji Mohammed Sani Musa, ya bayyana yadda ayyukan ‘yan ta’adda ke kara ta’azzara a yankinsa a matsayin abin damuwa.

A wata sanarwa da Sanatan ya sanyawa hannu, ya ce kananan hukumomi 5 cikin 9 da ke mazaɓarsa na fuskantar kawanya da matsin lamba daga ‘yan ta’adda.

Musa ya yi kira ga gwamnati da ta yi iya bakin kokarinta wajen ganin an dawo da zaman lafiya a yankin Neja ta Gabas.

Gwamnatin Zamfara Ta Dauki Nauyin Yaron da Yan Bindiga Suka Kashe Mahaifinsa

A wani rahoton kuma Gwamnatin jihar Zamfara ta ɗauki nauyin ƙaramin yaron nan da ya yi barzanar ɗaukar fansar kisan mahaifinsa.

Ma’aikatar Mata, Ƙananan yara da Ci gaban Jama’a ta jihar Zamfara ta yi alkawarin daukar nauyin karatun yaron da kuma walwalarsa ta yau da kullum.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262