Gwamnatin Zamfara Ta Dauki Nauyin Yaron da Yan Bindiga Suka Kashe Mahaifinsa
- Gwamnatin jihar Zamfara ta ɗauki nauyin ƙaramin yaron nan da ya yi barzanar ɗaukar fansar kisan mahaifinsa
- Uwar gidan gwamna Dauda Lawan na jihar, Hajiya Huriya Lawal, ta umarci kwamishinar mata ta nemo yaron da mahaifiyarsa
- Wani faifan bidiyon da ke yawo a soshiyal midiya ya nuna ƙaramin yaron yana cewa zai ɗauki fansa bayan yan bindiga sun kashe mahaifinsa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Zamfara - Ƙaramin yaron nan ɗan shekara 6 da faifan bidiyonsa ke yawo a kafafen sada zumunta ya samu tallafi daga gwamnatin jihar Zamfara, Leadership ta ruwaito.
Ma’aikatar Mata, Ƙananan yara da Ci gaban Jama’a ta jihar Zamfara ta yi alkawarin daukar nauyin karatun yaron da kuma walwalarsa ta yau da kullum.
Ƙaramin yaron dai ya nuna alhininsa kan kisan da aka yi wa mahaifinsa tare da yin barazanar daukar fansa kan 'yan bindiga da suka kashe masa mahaifi.
Kwamishinar mata, ƙananan yara da ci gaban jama'a, Dakta Nafisa Muhammad Maradun ce ta bayyana matakin gwamnatin Zamfara na ɗaukar nauyin yaron.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Da take jawabi ga manema labarai a Ofishinta da ke Gusau, kwamishinar ta ce gwamnatin Dauda Lawal ta shiga damuwa bisa halin da yaron ya tsinci kansa.
Ta ƙara da cewa matar mai girma gwamnan Zamfara, Hajiya Huriya Lawal, ta umarci ma'aikatar mata da ƙananan yara ta lalubo yaron da mahifiyarsa domin a taimaka musu.
Wane hali ƙaramin yaron ke ciki a yanzu?
"A halin da ake ciki, yaron yana samun shawarwari daga kwararru domin inganta rayuwarsa da saita masa tunani don gujewa abin da ka iya tasowa a nan gaba."
"Haka nan kuma mun tallafa wa mahaifiyarsa da jari mai gwabi wanda zata fara kasuwanci domin rage mata raɗaɗin halin da suka shiga."
- Dakta Nafisa Muhammad Maradun.
A nasa ɓangaren, ƙaramin yaron ya gode wa uwar gidan gwamnan jihar Zamfara da kwamishinar mata bisa karamci da taimakon da suka yi masa, rahoto ya tabbatar.
Gwamnatin Tarayya Ta Gayyaci NLC Da TUC Zuwa Taron Gaggawa a Abuja
A wani rahoton kuma Gwamnatin tarayya karkashin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ta kira taron gaggawa da shugabannin ƙungiyoyin kwadago NLC da TUC.
Rahotanni sun bayyana cewa taron zai gudana idan Allah ya kaimu an jima da yammacin yau Jumu'a, 29 ga watan Satumba, 2023 a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Asali: Legit.ng