Mahaifiyar Dr Zakeer, Young Sheikh Zaria Ta Riga Mu Gidan Gaskiya
- Allah ya yi wa mahaifiyar Dakta Zakeer wanda aka fi sani da Young Sheikh rasuwa a daren jiya a Zaria
- Marigayiyar ta rasu ne yayin haihuwa inda ta haifi ‘yan biyu mace da namiji kafin rasuwarta
- Mijin marigayiyar ya bayyana rasuwar tata a shafinsa na Facebook a yau Juma’a 29 ga watan Satumba
Jihar Kaduna – Ana cikin jimami yayin da mahaifiyar Dakta Zakeer wanda aka fi sani da Young Sheikh Zaria ta riga mu gidan gaskiya.
Dakta Zakeer ya bayyana rasuwar mahaifiyar tasa a shafinsa na Facebook a yau Juma’a 29 ga watan Satumba.
Yaushe mahaifiyar Young Sheikh ta rasu?
Ya ce mahaifiyar tasu ta rasu a cikin dare inda ya bayyana cewa za a yi sallar jana’izarta da misalin karfe 4:30 na yammacin yau Juma’a a Zawiyyar Sheikh Aliyu Mai Yasin a Zaria.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce ta rasu yayin haihuwa inda ta haifi ‘yan biyu mace da namiji kafin amsa kiran ubangiji.
Ya ce mahaifyar tasu ta rasu ta bar ‘ya’ya 10 wadanda su ka hada da kanne da yayu inda ya yi adduar ubangiji ya jikanta da rahama.
An gabatar da sallar jana'izar marigayar a yau Juma'a 29 ga watan Satumba da misalin karfe 4:30 ma yamma a Zaria.
Wanene Young Sheikh a fagen ilimi?
Yayin sanar da rasuwar mahaifiyar ta su, Young Sheikh ya bayyana cewa mahaifiyar tasu ta rasu ta bar su, su guda goma a gidan.
Young Sheikh ya kasace matashi kuma hazikin mai ilmantarwa a Najeriya wanda ya ke ba da gudunmawa a fannin ilimin addini.
Sai dai wasu da dama na korafin cewa Young Sheikh ya yi kankanta da zai hau mimbari don yin wa'azin addini, Daily Trust ta tattaro.
Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, Kungiyar Manyan Ma'aikatan Jami'o'in Najeriya Ta Yi Babban Rashi
Young Sheikh ya shafe shekaru da dama ya na wa'azi da kuma tafsirai inda ake yadawa a gidajen rediyo da talabijin.
Sheikh Giro Argungu ya riga mu gidan gaskiya
A wani labarin, Allah ya karbi rayuwar shehin malamin addinin Muslunci, Sheikh Giro Argungu da ke jihar Kebbi.
Shugaban Izala a Najeriya, Sheikh Bala Lau shi ya tabbatar da rasuwar malamin a shafinsa na Facebook.
Asali: Legit.ng