Mataimakiyar Sakataren SSANU Ta Kwanta Dama Sanasin Hatsarin Mota
- Ƙungiyar manyan ma'aikatan jami'o'in Najeriya ta yi babban rashi sanadin hatsarin mota ranar Alhamis, 28 ga watan Satumba
- Mataimakiyar babban sakataren SSANU na ƙasa, Esther Ezeama, ta mutu a haɗarin mota yayin da take hanyar zuwa jami'ar Maiduguri
- Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Kwamared Ibrahim, ya bayyana cewa sun yi babban rashin mace mai kwazo da aiki tuƙuru
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Mataimakiyar babban sakataren kungiyar manyan ma'aikatan jami'o'in Najeriya (SSANU), Esther Ezeama, ta rasu a wani hatsarin mota a ranar Alhamis.
Rahoton Daily Trust ya ce wani mummunar hatsari ya rutsa da ita a hanyar zuwa taron majalisar zartarwa na SSANU karo na 45 da aka gudanar jiya a jami’ar Maiduguri.
Shugaban ƙungiyar manyan ma'aikatan jami'o'in na ƙasa, Kwamared Mohammed Haruna Ibrahim, shi ya tabbatar da rasuwar Esther ga 'yan jarida.
Ya ce Esther ta rasa ranta ne a wata mota da ta ɗebo ma’aikatan sakatariyar SSANU ta kasa a wani wuri mai nisan kilomita 24 zuwa garin Bauchi a jihar Bauchi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mun yi babban rashi - SSANU
Ibrahim ya kuma bayyana cewa rasuwarta babban rashi ne ga kungiyar SSANU da kuma iyalan da ta rasu ta bari.
Shugaban ƙungiyar ya ƙara da bayanin cewa marigayiyar tana da kyawawan ɗabi'u, inda ya bayyana ta a matsayin mai tawali’u, mutuntaka, mai kwazo da uwa uba aiki tukuru.
A kalamansa ya ce:
"Kwanan nan ta aje aiki a jami'ar tarayya da ke Jos (babban birnin jihar Filato) inda ta kai matsayin Darakta kafin ta yi ritaya."
"Kuma ita mace ce da ta iya magana da harsunan ƙasashen waje kusan guda uku ban da yaren Hausa, Yarbanci da Igbo wanda ta iya a nan cikin gida."
Daga ƙarshe ya yi addu'ar Allah ya bai wa iyalanta haƙurin jure wannan rashi na farat ɗaya da suka yi ba zato ba tsammani, kamar yadda Naija News ta ruwaito.
Barazana Ga Alkalai: Da Gaske Za a Kama Kwankwaso? Sabbin Bayanai Sun Fito
A a wani rahoton na daban Wata ƙungiyar yaƙi da ta'addanci a Najeriya ta yi kira da a kama Sanata Kwankwaso bisa zargin yi wa alƙalai barazana.
Shugaban NCAT na ƙasa, Kwamared Terrence Kuanum, ya yi gargadin cewa akwai bukatar a dakile wuce gona da iri da 'yan Kwankwasiyya ke yi ba tare an taka musu birki ba.
Asali: Legit.ng