Bidiyon Ministan Abuja Wike Yana Girki Yayin da Gbajabiamila Ke Kallo Ya Yadu
- Sunan ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya sake hawa kanen labarai saboda wani bajinta da ya nuna
- An dauki bidiyon tsohon gwamnan na jihar Ribas yana girka abinci a kicin yayin da yake tare da abokansa a ranar hutu
- An gano Wike yana juya miya a cikin tukunya yayin da shugaban ma'aikatan shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ya tsaya yana kallo
Abuja - Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ya nunawa yan Najeriya cewa shi mutum ne da ya kware a bangarori daban-daban.
A cikin wani bidiyo da ya yadu a ranar Laraba, 27 ga watan Satumba, an gano tsohon gwamnan na jihar Ribas a cikin kicin yana baje kolin kwarewarsa a harkar girke-girke inda aka gano shi yana juya tukunyar miya.
An kuma gano tsohon kakakin majalisar wakilai kuma shugaban ma'aikatan shugaban kasa, Femi Gbajabiamila a cikin kicin din yana kallon yadda Wike yake girki.
Wike ya shiga sahun mutane kamar su Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun, wanda shima aka dauke shi a bidiyo yana baje kolin kwarewarsa a bangaren girki.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jama'a sun yi martani kan bidiyon Wike yana girki
A halin da ake ciki, yan Najeriya sun yi martani a kan bidiyon Wike yana girki tare da abokinsa Gbajabiamila a kicin.
A cikin da gajeren bidiyon, Mista Thomas Shelby OBE ya bayyana Wike a matsayin mutumin da ke da fasaha iri-iri.
Ya rubuta a shafinsa na X, @ChroniclesPHC:
"WIKE mutum ne mai fasaha iri-iri...."
@pretoriadaddyPya ce:
"Kalli tsohon gwamna na ya zama mai girki."
@ibadanguy ya ce:
"Hatta gbajabiamila bai manta cewa wike ne ke girki ba sai da ya tsaya kusa da shi a yayin da yake girki dole namiji ya tsaya kusa da shi yayin girkin duk da cewar ba komai yake yi ba."
@muels_SK ya ce:
"Mai gidan Abuja kan aiki."
"Litar Man Fetur Zata Karye Ta Dawo N180 a Najeriya" Fitaccen Malami Ya Fadi Lokaci
A wani labarin, shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele, ya bayyana cewa farashin man fetur zai fadi warwas daga N617 kan kowace lita a yanzu zuwa N180.
Ayodele wanda ya yi hasashen a cikin wani sabon bidiyo ya bukaci yan Najeriya da su sa rai da hakan.
Asali: Legit.ng