Ogun: DSS Ta Kama Dan Majalisar PDP Bisa Zargin Hannu a Kashe-Kashe
- Hukumar DSS ta kama mamban majalisar dokokin jihar Ogun da wasu mutum 5 bisa zargin hannu a kashe rayuka sama da 20 a Sagamu
- Jami'an tsaron farin kaya suna zargin ɗan majalisar na jam'iyyar PDP da hannu a rura wutar rikicin ƙungiyoyin asiri
- Jam'iyyar PDP ta tabbatar da kama ɗan majalisar, amma ta nuna rashin jin daɗinta da matakin DSS
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Ogun - Hukumar tsaron farin kaya (DSS) ta damƙe ɗan majalisar dokokin jihar da wasu mutane biyar bisa zargin hannu a kashe-kashen rayuka a jihar Ogun.
Jami'an DSS sun kama waɗanda ake zargin ne bisa zargin hannu a kashe rayukan mutane sama da 20 a rikicin ƙungiyoyin asirin da ya afku a Sagamu.
Wakilin Daily Trust ya tattaro cewa ɗan majalisar mai suna, Damilare Bello, shi ne mamba mai wakiltar mazaɓar Sagamu a majalisar dokokin jihar Ogun.
Hukumar DSS ta kama Honorabul Bello tare da Debbo Animashaun, Bamidele Saheed, Ismaila Onitire, Adewale Otesanya da kuma Tobi Owoade.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
An kuma tattaro cewa an kama dan majalisar wanda aka zaba a karkashin jam’iyyar PDP bisa zarginsa da hannu a rura wutar rikicin.
PDP ta yi Allah wadai da kama Honorabul Bello
Jam’iyyar PDP ta tabbatar da cewa jami'an DSS sun cafke Bello a cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai, Akinloye Bankole, ya fitar a Abeokuta.
Sai dai PDP ta yi Allah wadai da kama ɗan majalisar, inda ta ce:
"Duk da bamu adawa da matakin DSS ko wata hukumar tsaro na gudanar da bincike kan kashe-kashen Sagamu wanda ake zargin an kashe sama da mutane 25, muna ganin babu kwarewa da gaskiya a binciken da aka yi."
Haka nan kuma jam'iyyar ta ce babu wani makami ko wani abu na aikata laifi da aka samu a gidan Bello, An shafa masa kashin kaji ne domin ɓata masa suna a idon jama'a, Leadership ta ruwaito.
Kotun Zabe Ta Tsige 'Yan Majalisar Wakilan Tarayya 25 Da Sanatoci 5 Na Jam'iyyun APC, PDP, LP da NNPP
Tashin Hankali Yayin da Aka Kashe Sojoji da 'Yan Sanda da Yawa a Jihar Imo
A wani rahoton na daban Yan bindiga sun yi wa tawagar jami'an Soji, 'Yan sanda da Sibil defens kwantan ɓauna, sun halaka aƙalla 8 a jihar Imo.
Rahotanni daga mazauna yankin sun nuna cewa maharan sun ƙone jami'an tsaron har lahira a cikin motoci guda biyu.
Asali: Legit.ng