Uwargidan Shugaba Tinubu Ta Bukaci Yan Najeriya Mazauna Kasashen Waje Su Dawo Gida

Uwargidan Shugaba Tinubu Ta Bukaci Yan Najeriya Mazauna Kasashen Waje Su Dawo Gida

  • Uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu, ta yi kira ga ƴan Nijeriya mazauna ƙasashen waje da su dawo su gyara ƙasar nan
  • Ta yi wannan kiran ne ne a lokacin da take jawabi a wajen taron bunkasa tattalin arziƙin Najeriya da cinikayya a birnin New York na ƙasar Amurka
  • Remi Tinubu ta ce gwamnatin shugaba Tinubu na fatan aiwatar da gyare-gyare a fannin tattalin arziƙin Najeriya

New York, Amurka – Uwargidan shugaban ƙasa Bola Tinubu, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi kira ga ƴan Najeriya da ke ƙasashen waje da su dawo gida su shiga cikin shirin 'sabunta fata' na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Jaridar TheCable ta rahoto cewa uwargidan shugaban ƙasar ta yi wannan kiran ne a ranar Litinin, 18 ga watan Satumba, a birnin New York na ƙasar Amurka, a wajen taron bunƙasa tattalin arziƙin Najeriya da cinikayya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Shugaba Tinubu da NLC Sun Tashi Baram-Baram a Taron da Suka Yi, Bayanai Sun Fito

Remi Tinubu ta bukaci yan Najeriya mazauna kasashen waje su dawo gida
Remi Tinubu na son yan Najeriya mazauna kasashen waje su dawo gida domin bunkasa Najeriya Hoto: The Time is Now
Asali: Twitter

Ƙungiyar matan gwamnonin Najeriya ce ta shirya taron kuma an gudanar da shi a daƙin taro na Nigerian House da ke birnin New York.

Da take jawabi ga mahalarta taron, uwargidan shugaban ƙasar ta ce Najeriya na buƙatar gogewar ƴan kasarta da ke ƙasashen wajen domin su taimaka wajen ganin an cimma ƙudirin "sabunta fata".

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Uwargidan shugaban kasar ta ce:

"...dole ne mu himmatu wajen samar da yanayi mai kyau na samar da abubuwan buƙata na yau da kullum da za su bunƙasa cigaban al'umma ta hanyar samar da ingantaccen ilmi, yanayin samar da ayyukan yi, sannan bunƙasa masana’antu na cikin gida zai samar da ƙofofin cigaban tattalin arziƙi."
"Shirin sabunta fata wani shiri ne da muka fara, da nufin samar da ingantacciyar rayuwa ga iyalai."

Remi Tinubu ta yi alkawarin ba mata da matasa fifiko

Kara karanta wannan

Yan Soshiyal Midiya Sun Taso Obasanjo a Gaba Bayan Ya Yi Wa Sarakuna Wani Abu 1 a Bainar Jama'a

Uwargidan shugaban ƙasar ta bayyana cewa shirin "sabunta fata" yana da yawa kuma zai ba da fifiko ga yin gyare-gyare a sassa daban-daban kamar noma, ilimi, ƙarfafa tattalin arziƙi, kiwon lafiya da zuba jari, mata da matasa.

Ta kuma bukaci matan gwamnoni da su taka rawar gani yadda ya kamata domin samar da damammaki daidai da daidai ga al’ummar mata a Najeriya, domin hakan zai taimaka wajen kawar da mummunan yanayin ficewa daga ƙasar da ake yi.

Remi Tinuɓu Ta Yi Muhimmin Kira Ga Yan Najeriya

A wani labarin kuma, uwargidan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ta bayyana cewa lokacin jiran sai gwamnati ta yi komai a ƙasar nan ya wuce.

Remi Tinubu ta yi kira ga ƴan Najeriya da su tashi tsaye su daina kalmashe ƙafafuwansu suna jiran sai gwamnati ta yi musu komai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng