Gwamnan Jihar Osun Ya Sanya Dokar Kulle a Kananan Hukumomi 2 Na Jihar

Gwamnan Jihar Osun Ya Sanya Dokar Kulle a Kananan Hukumomi 2 Na Jihar

  • Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ya sanya dokar kulle a wasu ƙananan hukumomin jihar guda biyu
  • Sanya dokar kullen ya biyo bayan rikicin da ya ɓarke a tsakanin wasu ƙauyuka biyu na ƙananan hukumomin
  • Kolapo Alimi, kwamishinan watsa labarai na jihar ya bayyana cewa dokar kullen za ta riƙa aiki ne a tsakanin ƙarfe 8:00 na dare zuwa ƙarfe 6:00 na safe

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Osun - Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, a ranar Lahadi, 17 ga watan Satumba, ya sanya dokar kulle a ƙananan hukumomin Orolu da Irepodum na jihar.

Gwamnan ya sanya dokar kullen ne sakamakon rikicin da ya ɓarke kan filaye a tsakanin ƙauyukan Ilobu da Ifon, na ƙananan hukumomin, cewar rahoton PM News.

Gwamnan Osun ya sanya dokar kulle
Gwamna Adeleke ya sanya dokar kulle a kananan hukumomi biyu na Osun Hoto: Governor Ademola Adeleke
Asali: Facebook

Kwamishinan watsa labarai da wayar da kan jama’a na jihar, Kolapo Alimi, shi ne ya bayyana sanya dokar kullen a cikin wata sanarwa.

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo Ya Sanya Labule Da Tinubu? Gaskiya Ta Bayyana

Meyasa gwamna Adeleke ya sanya dokar?

Ya bayyana cewa an sanya dokar kullen ne biyo bayan rikicin da ya auku a tsakanin mutanen ƙauyukan Ilobu da Ifon domin tabbatar da doka da oda.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cikin sanarwar, kwamishinan ya bayyana cewa dokar za ta fara aiki ne daga ƙarfe 8:00 na kowane dare zuwa ƙarfe 6:00 na safe, rahoton TheCable ya tabbatar.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Hankalin gwamnatin jihar Osun ya kai kan rikicin filaye da ya ɓarke a tsakanin al'ummar ƙauyukan Ilobu da Ifon."
"A dalilin hakan ne gwamna Ademola Adeleke ya bayar da umarnin sanya dokar hana fita nan take a ƙananan hukumomin Orolu da Irepodun."
"Dokar kullen za ta fara aiki ne a tsakanin ƙarfe 8:00 na kowane dare zuwa ƙarfe 6:00 na safe. Domin haka an hana zirga-zirgar mutane da ababen hawa yayin dokar kullen har sai abin da hali ya yi."

Kara karanta wannan

Yan Soshiyal Midiya Sun Taso Obasanjo a Gaba Bayan Ya Yi Wa Sarakuna Wani Abu 1 a Bainar Jama'a

Kwamishinan ya kuma ƙara da cewa duk wanda aka samu da laifin karya dokar, za a kama shi tare da gurfanar da shi gaban kuliya.

Gwamna Ya Sanya Dokar Kulle

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Akwa Ibom, Bassey Otu, ya sanya dokar kulle a wasu ƙauyuka gudu huɗu na jihar.

Gwamnan ya sanya dokar ne biyo bayan rikicin filaye da iyakoki ya ɓarke a tsakanin ƙauyukan masu makwabtaka da juna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng