“’Ya'ya Maza Nake Haifa Ba Mata Ba”: Matar Aure Ta Yi Tinkaho a Yayin da Ta Je Ganin Filayen Mijinta

“’Ya'ya Maza Nake Haifa Ba Mata Ba”: Matar Aure Ta Yi Tinkaho a Yayin da Ta Je Ganin Filayen Mijinta

  • Wata mata yar Najeriya ta haddasa cece-kuce bayan ta wallafa wani bidiyo a shafinta na TikTok
  • Bidiyon ya nuno ta tare da surukinta yana nuna mata cikin kauyen da kuma filayen mijinta
  • Yayin da take wallafa bidiyon, matar ta yi tinkaho cewa 'ya;'ya maza kawai take haifa ba mata ba

Wata mata yar Najeriya mai suna @trinanicholas a TikTok ta sha caccaka a dandalin na soshiyal midiya saboda wani wallafa da ta yi a baya-bayan nan.

A cikin bidiyon, matar ta nuna farin cikinta a kan haihuwar 'ya'ya maza zalla da take yi.

Yar Najeriya ta yi murnar haihuwar yara maza zalla
“’Ya'ya Maza Nake Haifa Ba Mata Ba”: Matar Aure Ta Yi Tinkaho a Yayin da Ta Je Ganin Filayen Mijinta Hoto: @trinanicholas/TikTok.
Asali: TikTok

Wani mutum ya dauki surukarsa don nuna mata filayen mijinta

Wani bidiyo ya nuno matar tana tafiya tare da surukinta wanda ya ware lokaci don nuna mata filaye daban-daban da mijinta ya mallaka cike da jin dadi.

Kara karanta wannan

“Maza Guduna Suke Yi”: Budurwa Mai Katon Hanci Ta Koka, Ta Zubar Da Hawaye Saboda Rashin Mashinshini

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ta wallafa bidiyon a soshiyal midiya sannan ta jaddada muhimmancin haihuwar 'ya'ya maza ga mata.

Kalamanta:

"Surukina yana zagawa da ni don ganin dukka filayen mijina. 'Ya'ya maza na haifa a gida ba mata ba. Ba abu mai sauki bane ganin mata irina fa. A matsayinki na mace da bata da 'da namiji, ki kara kaimi wajen adu'a."

Jama'a sun yi martani kan bidiyon a TikTok

@lightetusi003 ta ce:

"Akwai wani fadi cewa idan ka tarbiyantar da diya mace, ka tarbiyantar da al'umma gaba daya? Ra'ayin son haihuwar 'ya'ya maza ya zama tsohon yayi yar'uwa."

@ijeomaikezuta bayyana:

"A gaba ne za mu san da namiji da diya mace wannene ya fi, ina alfahari da diyata."

@foski_draino ya yi martani:

"Lokacin da iyayen Bobrisky suka haife shi sun ji dadi cewa sun haifi namiji."

Kara karanta wannan

“Kana Da Kyau”: Wata Uwa Ta Roki Kyakkyawan Saurayi Da Ya Taimaka Ya Auri Diyarta

@desmondbum ta ce:

"Ba ku fahimceta ba, ba wai tana kaskantar da wadanda suke da yara mata bane, watakila a wajen mijinta, sun fi son da namiji fiye da 'ya mace."

@ellamara02 ta yi martani:

"Hajiya da yadda wasu matan ke jan akalar wasu 'ya'ya mazan kada ki yi tunkaho da wadannan yara mazan kada su bar ki a baya idan suka yi aure."

Wata uwa ta yi karin haske ga masu tunanin diyarta yar tsana ce

A wani labari na daban, wata uwa ta yi martani ga martani mara dadi da take samu daga jama'a game da diyarta.

Mutane da dama da suka ci karo da hotunan yarinyar a Instagram sun ce lallai yarinyar ba mutum bace, cewa yar tsana ce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng