Nasir El-Rufai Ya Yabi Wa'adin Mulkin Obasanjo Na Biyu
- Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana cewa a lokacin mulkin Obasanjo ne ƙasar nan ta koma kan tsari mai kyau
- A shekarar 2019, Obasanjo (wanda aka fi kira da OBJ) ya yabi El-Rufai a matsayin ɗaya daga cikin mutanen da ya ji daɗin aiki da su
- El Rufai a mayar da biki inda ya yabi tsohon ubangidan na sa a wajen wani taro a ranar Juma'a, 15 ga watan Satumba
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan jihar Ƙaduna, ya bayyana wa'adin mulki tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo na biyu (2003-2007), a matsayin wanda ya fi kowane nasara a tarihin ƙasar nan.
El Rufai ya yabi wa'adin mulkin na Obasanjo ta fannin samar da ayyukan yi, tattalin arziƙi, da raguwar hauhawar farashin kayayyaki.
El-Rufai ya yi aiki a ƙarƙashin gwamnatin Obasanjo na shekara takwas, a matsayin Darekta-Janar na hukumar Bureau for Public Enterprises (BPE), sannan daga baya a matsayin ministan babban birnin tarayya Abuja (FCT).
El Rufai ga yaba wa Obasanjo
A cewar rahoton The Cable, jigon na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ya bayyana cewa Najeriya ta koma kan tsarin da ya dace sannan mun samu sa'a a wa'adin mulkin Obasanjo na biyu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Da yake magana a ranar Juma'a, 15 ga watan Satumba a wajen taron 'Africa In the World' a birnin Stellenbosch, na ƙasar Afirika ta Kudu, El-Rufai ya bayyana cewa akwai buƙatar tsare-tsare masu kyau ga duk ƙasar da ke da niyyar bunƙasa.
A kalamansa:
"Idan aka duba yanayin tattalin arziƙin Najeriya, lokaci mafi nasara na shekara huɗu zuwa biyar na bunƙasar tattalin arziƙi, samar da ayyukan yi, da rage hauhawar farashin kayayyaki, shi ne lokacin wa'adin mulkin shugaba Obasanjo na biyu a shekarar 2003 zuwa 2007, inda a karon farko ƙasar ta koma kan ingantaccen tsari kuma muka samu sa'a."
"Farashin man fetur ya fara hauhawa amma ba mu barnatar da shi ba saboda mun shirya. Muna da asusun rarar ribar kuɗin man fetur (ECA) wanda ya dogara ne kan tsarin kasafin kudi cewa duk wani rarar da aka samu sama da wani ma'auni na farashin ɗanyen man zai tafi kai tsaye zuwa asusun ajiyar."
Obasanjo Ya Umarci Sarakuna Su Gaida Shi
A wani labarin kuma, tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya janyo cece-kuce bayan ya umarci sarakunan Yarbawa na gargajiya su miƙe su gaida shi a wajen wani taro.
Tsohon shugaban ƙasan an nuna shi a cikin wani faifan bidiyo yana tsawatar wa ga sarakunan kan yakamata su girmama wanda ya cancanci a girmama shi.
Asali: Legit.ng