“Kana Da Kyau”: Wata Uwa Ta Roki Kyakkyawan Saurayi Da Ya Taimaka Ya Auri Diyarta

“Kana Da Kyau”: Wata Uwa Ta Roki Kyakkyawan Saurayi Da Ya Taimaka Ya Auri Diyarta

  • Wani mutum wanda ya halarci shagalin bikin aure ya ce wata mata ta tunkare shi sannan ta fada ma shi cewa tana da diya da bata yi aure ba
  • Mutumin ya ce auren abokinsa ya je, sannan matar ta hadu da shi bayan an gama taron tare da gabatar masa da bukatarta
  • Ya wallafa wani bidiyonsa tare da jinjinawa kyawunsa, cewa dalilin da yasa matar take so wa diyarta shi kenan

Wani mutumi ya ce ya halarci shagalin bikin abokinsa lokacin da wata uwa ta tunkare shi kan ya auri diyarta.

A cikin wani bidiyo da @moniibrizzy ya wallafa, mutumin ya yi ikirarin cewa matar ta ga yadda ya yi kyau sai ta yanke shawarar mika kokon bararta.

Wata uwa ta nemi kyakkyawan saurayi ya auri diyarta
“Kana Da Kyau”: Wata Uwa Ta Roki Kyakkyawan Saurayi Da Ya Taimaka Ya Auri Diyarta Hoto: TikTok/@moniibrizzy and Getty Images/Andreswd. An yi amfani da hoton matar don misali ne
Asali: UGC

Bidiyon ya nuno matashin zaune a bayan wata mota, yana magana da wasu da ba a nuno fuskarsu ba.

Kara karanta wannan

"Ban San Zaman Lafiya Ba Tunda Na Aureta": Magidanci Ya Roki Kotu Ta Raba Aurensa Mai Shekaru 51

Ya ce matar ta dage cewa har yanzu diyar tata bata da saurayi sannan ta tambaye shi ko zai aure ta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Uwa ta tunkari saurayi a madadin diyarta

Ya ce yarinyar da ake magana a kanta daliba ce a jami'ar jihar Imo, IMSU kuma cewa an nuna masa hotunanta.

An rubuta a jikin bidiyon:

"Na je auren mutumina. Bayan taron, lokacin da nake shirin wucewa, wata uwa ta zo garni sannan ta fada mani cewa tana sona kuma tana so na aure diyarta da ke karatu a jami'ar IMSU. Ta nuna mun hotunanta sannan ta bani lambarta. Mama na so wa diyarta abu mai kyau."

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani yayin da uwa ta nema wa diyarta auren kyakkyawan saurayi

@cassandrachristo8 ta ce:

"Abun yanzu shine, shin yarinyar tana so?"

Kara karanta wannan

"Sabuwa Fil a Leda": Ango Ya Nuna Zumudinsa Bayan Ganin Fuskar Amaryarsa a Daren Farko, Bidiyon Ya Yadu

@Don Giovanni ya yi martani:

"Yadda na hadu da matata."

@user1407713225572 ya ce:

"Ba karamin abu bane faaa. Mama na son abu mai kyau.

@user8189536774237 ta yi martani:

"Mama na son zuwa zaman jego mai kyau."

Wani mutum ya nemi kotu ta raba aurensu mai shekaru 51

A wani labarin, mun ji cewa wani mutum mai suna Ojo Olaoye, ya roki wata kotun gargajiya da ke Oja Oba, Mopa a Ibadan, jihar Oyo da ta raba aurensa mai shekaru 51 da matarsa Janet Olaoye.

Kamar yadda jaridar Nigerian Tribune ta rahoto, Ojo ya zargi matar tasa da taurin kai, yawan fada, tashin hankali da yin barazana ga rayuwarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng