Obasanjo Ya Umarci Sarakuna Su Mike Su Gaida Shi a Wajen Wani Taro a Jihar Oyo
- Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya zama abun magana a soshiyal midiya bayan an saki wani bidiyonsa
- An nuna tsohon shugaban ƙasan a cikin bidiyon yana umartar sarakunan gargajiya a jihar Oyo su miƙe su gaida shi
- Wannan lamarin dai ya auku ne a wajen ƙaddamar da titin hanyar Oyo-Iseyin mai tsawon kilomita 34.85 a ranar Juma'a
Iseyin, jihar Oyo - Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya sami kansa a cikin wani cece-kuce bayan wani abu da ya yi a wajen ƙaddamar da titin hanyar Iseyin-Oyo mai tsawom kilomita 34.85 a a ranar, Juma'a 15 ga watan Satumban 2023.
Obasanjo wanda gwamna Seyi Makinde ya gayyato, an kuma ba shi damar ƙaddamar da sabuwar harabar jami'ar fasaha ta Ladoke Akintola (LAUTECH) a Isiyen, wacce ke ɗauke da kwalejin noma da sabunta albarkatun ƙasa.
A wajen ƙaddamar da waɗannan ayyukan, tsohon shugaban ƙasan a cikin wani faifan bidiyo, an nuna shi cikin murtuke fuska lokacin da ya yi tsawatar wa ga sarakunan da suka halarci taron.
Obasanjo wanda ya yi magana cikin harshen Yarbanci, ya yaba wa sarakunan Oyo amma ya umarce su da su miƙe tsaye su gaida shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa yana da muhimmanci su girmama wanda ya cancanci a girmama shi a wajen taro irin wannan.
Obasanjo ya bayyana cewa dole ne basarake ya mutunta kasancewar gwamna ko shugaban ƙasa a wajen kowane irin taro ne.
A kalamansa:
"A al'adar Yarbawa, muna girmama abubuwa biyu da sauransu: shekaru da matsayi. Matsayin gwamna ya fi na kowane sarki girma."
"Ko a lokacin da nake shugaban ƙasa, ina duƙa wa don girmama sarakuna. Amma a cikin ɗaki, sarki ne ke duƙa min."
Wane irin martani ƴan soshiyal midiya suka yi?
@Olahitan0 ya rubuta:
"Shirme kawai ka ce mu mutunta al'adarmu amma ka raina sarkinmu. Sarakuna mutane ne da ake girmama su ta yadda mahaifiyar sarki har ɗuka wa take ta gaida shi da ya zama sarki, yanzu an daina mutunta sarakuna a ƙasar Yarbawa."
Idris Ayodeji. K. ya rubuta:
"Sarakunan siyasa."
@Ebirigbonka ya rubuta:
"Wannan kuskure ne."
Abokin Adawar Buhari Ya Samu Mukami
A wani labarin kuma, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya ba wanda ya yi takara da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, a zaɓen 2019, shirgegen muƙami.
Mista Tope Fasua ya yi magana a shafin X wanda aka fi sani da Twitter, ya ce ya zama mai bada shawara ga gwamnatin tarayya.
Asali: Legit.ng