“Za Mu Kashe Biliyan 5 Wajen Gyara Ofishin Gwamna”: Gwamnan Cross River Ya Fadi Dalili
- Gwamnan jihar Cross River, Bassey Otu ya bayyana ainahin kudin da ake bukata don gyara ofishinsa
- Gwamnan ya bayyana cewa yana bukatar naira biliyan 5 don gyara ofishoshinsa a Abuja, Lagas da sauran wurare
- A cewar Otu, ofishin gwamnan bai kai yadda zai jawo hankalin masu zuba jari da ke son kasuwanci da jihar ba
Jihar Cross River - Gwamnan jihar Cross River, Bassey Otu, ya bayyana cewa zai kashe kimanin naira biliyan 5 wajen gyara ofishin gwamnan jihar da ke Calabar, babban birnin jihar don ya fi yadda yake a yanzu.
Gwamna Otu ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a, 15 ga watan Satumba, yayin tattaunawa da manema labarai a jihar, cewa ya kamata ofishin gwamna ya zama alama a jihar.
Kotun Zabe: Kwamishina Ya Yi Barazanar Kisa Ga Alkalai, Ya Ce Kano Za Ta Shiga Masifa Fiye Da Zamfara, Katsina
Dalilin da yasa zan gyara ofishin gwamna da biliyan 5 - Bassey Otu
Gwamnan ya ce zai kuma gyara dukkan ofisoshin jihar da ke Abuja, Lagas da sauran wurare don su kasance dauke da tambari iri daya, yana mai cewa ofishin gwamnan baya cikin saiti a lokacin da ya karbi mulki, , Rahoton Sahara Reporters.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Har ila yau, gwamnan ya kuma bayyana cewa gyara ofishin da kyau zai taimaka wajen jawo hankalin masu zuba hannun jari da ke son yin kasuwanci da jihar.
Jaridar PM News ta nakalto Otu yana cewa:
"Ba zan daina kashe kudi don gyara ofishin gwamna ya dawo saiti ba. Ya kamata ya zama alamar jihar. Zan yi irin haka a dukkan ofisoshinmu na hadin gwiwa.
"Lokacin da ka gyara mazauninka ko ofishinka ya zama cikin saiti ne zai kara maka daraja sannan ya ja hankalin masu zuba jari. Kazantar wuri da gine-gine marasa kyau zai iya sanyaya gwiwar mutane.
"Za a yi gyare-gyaren cikin gaskiya. An kiyasta cewa aikin gyaran zai ci tsakanin biliyan 3 zuwa 5. Amma a halin yanzu yan kwangilar suna aiki tukuru."
Ganduje, Gwamnonin APC da Wasu Jiga-Jigai Sun Dira Jihar Imo
A wani labarin, mun ji cewa shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, wasu gwamnoni da mataimakin kakakin majalisar wakilai, sun dira Owerri, babban birnin jihar Imo.
Manyan ƙusoshin jam'iyyar APC na ƙasa sun mamaye Imo da ke Kudu maso Gabashin Najeriya ranar Jumu'a domin kaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen gwamna.
Asali: Legit.ng