Ginin Bene Mai Hawa 20 da Ake Gina Wa Ya Ruguje Kan Jama'a a Delta

Ginin Bene Mai Hawa 20 da Ake Gina Wa Ya Ruguje Kan Jama'a a Delta

  • Mutane da dama sun samu raunuka yayin da wani gini mai hawa 20 ya kife a Asaba jihar Delta da yammacin Alhamis
  • Ganau sun bayyana cewa lamarin ya faru ba zato ba tsammani yayin da ma'aikata ke ci gaba da aikin ginin
  • Kwamishininan sabunta birane na gwamnatin jihar Delta ya ce sun fara gudanar da bincike don gano ainihin abinda ya faru

Delta - Wani ginin bene mai hawa 20 da ake aikin ginawa ya ruguje a Asaba, babban birnin jihar Delta, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

A cewar wani ganau da ibtila'in ya auku a kan idonsa, lamarin ya yi sanadin raunata mutane kusan takwas ranar Alhamis, 14 ga watan Satumba, 2023.

Ginin Otal mai hawa 20 ya faɗo.
Ginin Bene Mai Hawa 20 da Ake Gina Wa Ya Ruguje Kan Jama'a a Delta Hoto: leadership
Asali: UGC

Ginin otal ɗin na biliyoyin Naira da ke daura da Delta Mall ya ruguje ne da yammacin ranar Alhamis yayin da ma'aikata ke tsaka da aiki.

Kara karanta wannan

Ana Binciko Mutanen da ke da Alaka da Emefiele a Badakalar Naira Tiriliyan 7 a CBN

An tattaro cewa ginin otal ɗin mallakin hamshakin attajirin dan kasuwa ne kuma wanda ya kafa kamfanin RainOil Group, Cif Gabriel Ogbechie.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jami’an hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Delta da jami’an tsaro sun kewaye wurin da lamarin ya faru a halin yanzu, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

Mutun nawa rushewar ginin ta shafa?

Wata shaidar gani da ido ta ce ita da wasu da ke kasuwanci a kusa da wurin sun yi mamakin yadda kwatsam suka ji kara yayin da ma’aikatan ke tsaka da aikin ginin.

Matar, wacce ta bayyana sunanta da, Onyinye Okei, ta ce kusan ma'aikata Takwas suka samu raunuka kuma tuni abokan aikinsu suka garzaya da su Asibiti.

Me ya haddasa rugujewar ginin?

Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala duba ginin da ya ruguje, kwamishinan sabunta biranen jihar, Mista Michael Anoka, ya ce lamarin ya faru ne sakamakon rashin ingancin ginin.

Kara karanta wannan

Hatsarin Kwale-Kwale a Neja: Adadin Wadanda Suka Mutu Ya Karu Zuwa 30, NSEMA

Anoka, wanda ya tabbatar babu wanda ya mutu, ya ce:

"Muna kan aikin bincike don gano musabbabin faruwar lamarin kuma gwamnati ta fara daukar matakai kamar yadda kuke gani an rufe wurin. Bayan mun gama bincike, zamu faɗi rahoton abinda muka gano."

Ko da gaske ne Tinubu zai kafa sabuwa ma'aikata?

A wani labarin kuma Bola Ahmed Tinubu ya sha alwashin kawo karshen faɗace-faɗace tsakanin manoma da makiyaya a faɗin Najeriya.

Sai dai kwamitin da aka kafa na sake fasalin kiwon dabbobi bisa jagorancin Ganduje ya shawarci shugaban ƙasa ya kafa ma'aikatar dabbobi domin aiwatar da abubuwan da suka gano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262