Tsohon Shugaban Hukumar FIRS Da Tinubu Ya Tsige Ya Magantu
- Tsohon shugaban hukumar tara haraji ta kasa (FIRS), Mohammad Nami, ya yi martani a kan tsige shi da Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi
- Mutumin mai shekaru 55 ya yi godiya ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da shugaban kasa mai ci Bola Ahmed Tinubu kan ba shi damar hidimtawa kasa
- Ya ce gwamnatinsa ta tara naira tiriliyan 8 cikin watanni takwas kuma kuma ya ji dadin cika ayyukan sa
FCT, Abuja - Muhammad Nami, tsohon shugaban hukumar tara haraji ta kasa (FIRS), ya yi martani a kan sauke shi da aka yi daga kujerarsa.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya tsige Nami a ranar Alhamis, 14 ga watan Satumba sannan ya nada mai ba shi shawara ta musamman kan kudaden shiga, Zacchaeus Adedeji, a matsayin mukaddashin shugaban hukumar harajin.
A wanni bayan tsige shi, Nami ya fitar da sanarwa inda ya yi godiya ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan ba shi damar hidimtawa kasa.
Nami ya kuma mika godiyarsa ga ma'aikatan FIRS wadanda suka yi aiki tare da shi tsawon shekarun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya rubuta:
“Cike da matukar godiya ga Allah Madaukakin Sarki, ina so in mika sakon godiyata ga tsohon shugaban kasa, Mai Girma Muhammadu Buhari GCFR, da kuma shugaban kasa mai ci, Bola Ahmed Tinubu GCFR, kan damar da aka bani na yi wa kasa da al'umma hidima a matsayin shugaban hukumar tara haraji ta kasa (FIRS) na kusan shekaru hudu.
"Ina son mika tsantsar godiyata ga daukacin ma'aikatan hukumar, masu biyan harajinmu, da kuma yan Najeriya kan yarda da suka yi da ni da maramun baya da bani hadin kai iya lokacin da na yi a mulki."
FIRS ta tara naira tiliyan 8 cikin wata takwas a karkashin gwamnatina - Nami
Nami ya kuma jaddada nasarorin da ya samu a yayin kula da ragamar harkokin lamura a matsayin shugaban FIRS.
Ya ce gwamnatinsa ta tara naira tiriliyan 8 cikin watanni takwas kuma da za ta sake kafa sabon tarihi na tara akalla naira tiriliyan 13 zuwa karshen shekara.
Nami ya ce zai bar hukumar FIRS a matsayin wanda burinsa ya cika bayan ya cimma duk abubuwan da ya sa gaba a lokacin da yake aiki a matsayin shugaban FIRS.
Ya ce:
"Saboda haka, zan iya cewa zan tafi a matsayin mutum mai cikar buri sanin cewa na yi aiki yadda ya kamata. Zan kuma bar aikin da aka gina bisa inganci na duniya."
Tinubu ya nada Delu Yakubu a matsayin shugabar hukumar NSIPA
A wani labarin, mun ji cewa shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Delu Bulus Yakubu a matsayin shugabar Hukumar Jin Dadin Al'umma ta Kasa (NSIPA).
Daga Villa Zuwa Gonar Daura: Shehu Ya Bayyana Sabon Aikin Buhari Kwana 100 Bayan Barin Fadar Shugaban Kasa
Wannan nadin nata zai tabbata ne idan majalisar Dattawa ta tantance ta tare da tabbatar da mukamin nata, Legit ta tattaro.
Asali: Legit.ng