Kashin Manya Da Yawa Zai Bushe da Binciken Godwin Emefiele Ya Shiga Wasu Hukumomi
- Tun da Bola Ahmed Tinubu ya shiga Aso Rock Villa, wasu ma’aikatan CBN su ka shiga dar-dar
- Shugaban kasa ya dakatar da Gwamnan bankin CBN watau Godwin Emefiele, kuma ana bincikensa
- Binciken da Jim Obazee yake yi zai shafi hukumar NIRSAL inda ake zargin an wawuri wasu kudi
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Jami’in da Bola Ahmed Tinubu ya kawo musamman domin ya yi bincike a kan ayyukan CBN ya shirya fara tasa keyar ma’aikatan bankin.
Rahoton da aka samu a Daily Trust ya nuna Jim Obazee zai fara tsare manyan jami’ai ya na yi masu tambayoyi kan zargin ba dai-dai ba da aka yi.
Jami’in ‘dan sandan da aka ba Jim Obazee domin ya taimaka masa da binciken, DCP Eloho Edwin Okpoziakpo ya hana wasu jami’an gwamnati barci.
Badakala a hukumar NIRSAL
Sauran jami’an tsaron kwamitin su ne CSP Celestine Odo; CSP Segun Aderoju da DSP Tijani A. Bako kamar yadda ku ka ji a wani rahoto da mu ka kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Binciken da ake yi zai shafi hukumar NIRSAL musamman a kan abubuwan da su ka faru a kafin shugaban kasa ya tsige Aliyu Abbati Abdulhameed.
Akwai badakalar kwangilar alkamar Naira biliyan 5.6 a Kano da Jigawa, sannan an rika kashe N600, 000 a wata a kula da karnukan tsohon shugaban.
Rahoton ya ce za a taso na kusa da Godwin Emefiele a game da wasu kwangiloli da aka bada a NIRSAL da kuma tsarin noman shinkafa da aka kawo.
CBN ya bada wasu kwangiloli
Wata kwangila da ta jawo alamar tambaya ita ce wanda aka ba kamfanin Syspec Network Limited domin tattaro sunayen masu zaman banza a Jigawa.
Binciken zai tabo yadda mutanen tsohon gwamnan bankin CBN su ka boye kudi a akawun dinsu domin samun riba, za ayi amfani da su ne wajen noma.
Jinkirin fitar da kudin da aka yi ya jawo bata lokaci wajen samun takin zamani da iri a kan kari, ana zargin hakan ya yi tasiri a lokacin noman damina.
Babu mamaki saboda haka ne ake zargin ma’aikatan NIRSAL sun lalata takardun da ke ofisoshin wadanda za su iya zama hujjoji a wajen binciken nan.
Emefiele a badakalar N7tr
Ku na da labari kwamitin da aka kafa ya fara kokarin cafke na kusa da tsohon Gwamnan CBN a binciken da ake yi kan wawurar tiriliyoyin kudi.
Wannan kwamiti ya kama hanyar bankado wasu da ake zargi su na da hannu a satar makudan kudin da adadinsu zai iya kai Naira tiriliyan 7 a CBN.
Asali: Legit.ng