Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Ganduje da Hafsoshin Tsaro a Villa

Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Ganduje da Hafsoshin Tsaro a Villa

  • Bola Ahmed Tinubu ya gana da shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, da manyan hafsoshin tsaro a Aso Villa
  • Wakilan ƙungiyar fulani makiyaya ta ƙasa MACBAN sun halarci zaman wanda ya maida hankali kan muhimmin batu
  • Wasu majiyoyi daga fadar shugaban ƙasa sun nuna cewa mahalarta taron zasu tattauna kan yadda za a kawo karshen rikicin manoma da makiyaya

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na gana wa yanzu haka da tawagar wakilai ƙarƙashin jagorancin shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje a fadar shugaban ƙasa.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa taron, wanda aka shiga da misalin ƙarfe 3:00 na yammacin yau Alhamis, ya samu halartar hafsoshin tsaron ƙasar nan.

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Ganduje da Hafsoshin Tsaro a Villa Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa har zuwa loƙacin haɗa wannan rahoton, ba bayyana ajendar da taron zai maida hankali ba.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Naɗa Sabbin Shugabannin Hukumomi 2 Na Tarayya, An Faɗi Sunayensu

Duk da haka, wasu rahotanni sun bayyana cewa tawagar wakilan zata gabatar wa shugaban ƙasa kundin da ke kunshe da hanyoyin warware rikicin manoma da makiyaya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wakilan ƙungiyar fulani makiyaya ta Najeriya watau Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria, (MACBAN) sun halarci taron wanda ya gudana a fadar shugaban ƙasa.

Zubar da jini ya yi yawa tsakanin manoma da makiyaya

Tun daga shekarar 1999 zuwa yau, rikicin manoma da makiyaya a Najeriya ya lalume rayukan dubbannin 'yan Najeriya musamman a shiyyar Arewa ta Tsakiya.

A ranar 29 ga watan Agusta, 2023, kakakin majalisar wakilan tarayya, Tajudeen Abbas, ya ambabaci adadin mutanen da suka mutu sakamakon rikicin da dubu 60,000.

Abbas ya koka da cewa, rikicin manoma da makiyaya da ƙi ci ya ƙi cinye wa zuwa yanzu, wanda ake kallo a matsayin rikicin yanki, ya fasu zuwa kasashen yammacin Afirka da dama.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Gana da Gwamnan PDP Da Tawagar Masu Ruwa da Tsakin Jiharsa a Villa

Gwamnatin Bola Tinubu ta kafa kwamiti na musamman da zai lalubo hanyoyin kawo ƙarshen wannan rikici a faɗin sassan Najeriya.

Shugaba Tinubu Ya Gana da Gwamna Fubara da Wasu Masu Ruwa da Tsaki a Ribas

Rahoto ya nuna cewa Bola Ahmed Tinubu ya gana da masu ruwa da tsaki na jihar Ribas karkashin jagorancin gwamna Siminalayi Fubara.

Wannan gana wa, wacce ta gudana a fadar shugaban ƙasa da ke birnin tarayya Abuja, ta samu halartar Nyesom Wike, ministan Abuja kuma tsohon gwamnan jihar Ribas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262