Ministan Tinubu Ya Gana da Tsohon Shugaban Kasa Jonathan da Asari Dokubo
- Abubakar Momoh Ministan raya Neja Delta ya gana da tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan kan muhimman batutuwa a Abuja
- Wata sanarwa daga Ofishin ministan ta bayyana abubuwan da suka tattauna domin kawo ci gaba da yankin mai dumbin arziƙin man fetur
- Ministan ya kuma gana da Asari Dokubo a yunkurinsa na kawo karshen satar ɗanyen mai da gina Neja Delta
FCT Abuja - Ministan harkokin raya Neja Delta, Abubakar Momoh, ya gana da tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, domin tattauna batutuwan da suka shafi yankin Neja Delta.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa daga cikin abubuwan da suka tattauna harda batun yadda za a kawo ƙarshen satar ɗanyen mai da kuma lalata kayan gwamnati.
Ministan ya kuma gana da Asari-Dakubo a wani bangare na tuntuɓa da lalubo dabarun samar da mafita ga dimbin kalubalen da ke damun yankin mai arzikin man fetur.
Rahoto ya nuna cewa gangar man da Najeriya ke haƙowa a kowace rana ta faɗi ƙasa zuwa ganga 470,000 a watan Agusta, 2023, hakan na nufin kaso 23 cikin 100 ɓarayi ke sace wa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Muhimmin dalilin ziyarar da Ministan ya kai wa Jonathan
Ministan ya kai wa tsohon shugaban ƙasa Jonathan ziyara ta musamman domin neman shawarwarinsa kan yadda za a shawo kan baki ɗaya matsalolin da suka addabi yankin.
Wata sanarwa da ta fito daga ofishin ministan raya Neja Delta ta nuna cewa sun yi tattauna wa mai ma'ana da fahimta kan dabarun yaƙi da satar ɗanyen mai, gina ababen more rayuwa da samar da ayyuka ga matasa.
Wani ɓangaren sanawaran ya ce:
"A ranar Talata tsohon shugaban kasa, Dakta Goodluck Ebele Jonathan ya karbi bakuncin ministan a gidansa da ke birnin tarayya Abuja."
"Sun yi tattaunawa mai kima da fahimta, inda suka mai da hankali kan dabarun yaki da satar danyen mai, inganta ababen more rayuwa, da samar da ayyukan yi ga matasa a yankin Neja Delta."
Gwamna Sanwo-Olu Na Lagos Ya Rantsar da Kwamishinoni 37 da Hadimai
Rahoto ya nuna kwamishinoni 37 da masu bai wa gwamna shawara ta musamnan sun karbi rantsuwar kama aiki a jihar Legas.
An sha taƙaddama kan jerin sunayen kwamishinonin tsakanin gwamna Babajide Sanwo-Olu da majalisar dokokin jihar.
Asali: Legit.ng