Mambobin Kungiyar NURTW Sun Ba Hammata Iska a Abuja

Mambobin Kungiyar NURTW Sun Ba Hammata Iska a Abuja

  • Mutanen birnin tarayya Abuja sun shiga firgici a ranar Talata lokacin da mambobin NURTW suka yi rikici inda har bindigu aka harba
  • Shaidar ganau ba jiyau ba ya bayyana cewa ba zai iya tantance cewa ko bindigun da aka harba daga ƴan sandan ne ko daga mambobin ƙungiyar ba
  • An fahimci cewa rikicin ya auku ne a tsakanin shugaban ƙungiyar na ƙasa, Tajudeen Baruwa da magoya bayan Badru Agbede

FCT, Abuja - An shiga tashin hankali da firgici a birnin tarayya Abuja a ranar Talata, 12 ga watan Satumba, lokacin da tsagin ƙungiyar direbobin motocin sufuri ta ƙasa (NURTW) suka ba hammata iska.

Shaidar ganau ba jiyau ya tabbatar da cewa an yi harbe-harben bindiga a lokacin rikicin, cewar rahoton Channels tv.

Mambobin NURTW sun yi fada a Abuja
Mambobin NURTW sun sake ba hammata iska a Abuja Hoto: @OWallelle
Asali: Twitter

Shaidar gani da ido ya magantu kan rikicin NURTW a Abuja

Kara karanta wannan

Hawaye Sun Kwaranya Yayin Da Adadin Mutanen Da Girgizar Kasa Ta Halaka a Morocco Ya Karu Da Yawa

Da yake magana bayan ya nemi a sakaya sunansa, shaidar gani da idon ya bayyana cewa ba zai iya tabbatar da cewa bindigun da aka harba daga ɓangaren ƴan sanda ne ba, ko mambobin ƙungiyar masu faɗa da juna.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An tattaro cewa rikicin ya auku ne a tsakanin mambobin ƙungiyar da ke biyayya ga shugaban ƙungiyar na ƙasa, Tajudeen Baruwa, da magiya bayan abokin hamayyarsa Badru Agbede, rahoton Vanguard ya tabbatar.

Baruwa ya sha yin kira ga ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) da ta sanya baki domin a warware rikicin, ta yadda za a dawo da mambobinsa a hedikwatar ƙungiyar ta ƙasa wacce a yanzu haka take a ƙarƙashin ikon ƴan sanda.

Jami'an ƴan sanda har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton, ba su ce komai ba dangane da rikicin da ya auku.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 2 Sace Wasu Mutane Masu Yawa a Arewacin Najeriya

Abun sani dangane da rikicin NURTW a Abuja

Baruwa shi ne tsohon shugaban NURTW a jihar Ogun, yayin da Agbede ya riƙe muƙamin shugabancin ƙungiyar a jihar Legas

Kafin a zaɓe shi a karo na biyu, Baruwa ya samu saɓani da reshen ƙungiƴar na jihar Legas a ƙarƙashin shugabancin Musiliu Akinsanya wanda aka fi sani da MC Oluomo, inda suka fice daga ƙungiyar.

Ana Shirin Kai Hari a Sakatariyar NURTW

A baya labari ya zo kan yadda ƙungiyar direbobin motocin sufuri ta ƙasa (NURTW), ta nuna fargabar ta kan shirin da wasu ke yi na gudanar da zanga-zanga a sakatariyar ƙungiyar da ke Abuja.

Kungiyar ta yi bayanin cewa wasu mutane ke son ɓoyewa da zanga-zangar domin tayar da hankalin mazauna birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng