Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 2 Da Sace Wasu Mutum 7 a Jihar Kebbi
- Ƴan bindiga sun halaka mutum biyu tare da yin awon gaba da wasu mutum bakwai a ƙauyen Kwarikwarasa na jihar Kebbi
- Gwamnan jihar Kebbi ya ziyarci inda lamarin ya auku, sannan ya bayar da kyautar naira miliyan 10 ga waɗanda harin ya ritsa da su
- Gwamna Nasiru ya kuma sha alwashin magance matsalar tsaro a jihar inda ya ce gwamnatinsa na ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatuwar hakan
Jihar Kebbi - Ƴan bindiga sun kai hari a ƙauyen Kwarikwarasa na ƙaramar hukumar Maiyama a jihar Kebbi.
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa a yayin harin, ƴan bindigan sun halaka mutum biyu, sannan suka yi awon gaba da wasu mutum bakwai da ba su ji ba, ba su gani ba.
An tattaro cewa ƴan bindigan sun farmaki ƙauyen ne da safiyar ranar Asabar, inda suka aikata wannan ta'asar.
Ƴan bindigan daga baya sun sako ɗaya daga cikin waɗanda suka sace inda suka tafi da mutum shida ciki har da wata mace guda ɗaya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Gwamnan Kebbi ya ziyarci ƙauyen
Gwamnan jihar Kebbi, Nasiru Idris, ya ziyarci ƙauyen inda ya bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa ta ɗauki matakan da za su hana aukuwar hakan a nan gaba.
Gwamnan ya kuma bayar da kyautar naira miliyan 10 (N10m) ga iyalan waɗanda suka rasu tare da waɗanda suka samu raunika a harin, rahoton The Guardian ya tabbatar.
Ya bayyana cewa gwamnatinsa ta ba jami'an tsaro dukkanin goyon bayan da su ke buƙata domin daƙile ayyukan ta'addanci a jihar.
"Ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba har sai mun tabbatar da cewa mun tsare jihar nan ta yadda jama'a za su iya barci cikin kwanciyar hankali, su noma gonakinsu sannan su yi harkokin kasuwancinsu ba tare da fargaba ba."
Yan Daba Sun Halaka Jami'in 'Yan Sanda
A wani labarin kuma, wasu miyagun ƴan daba sun halaka wani babban jami'in ƴan sandan Najeriya mai matsayin DPO a jihar Rivers.
Miyagun ƴan daban sun halaka Bako Angbashim, DPO na ƴan sandan ƙaramar hukumar Ahoada ta Gabas, a wani bata kashi da suka yi bayan sun yi masa kwanton ɓauna tare da tawagarsa.
Asali: Legit.ng