Dan Achaba Ya Rasa Ransa a Wani Hatsari Da Motar Tirela a Jihar Kwara
- Wani ɗan Achaɓa ya rasa ransa a wani hatsari da ya ritsa da shi da wata babbar motar tirela a birnin Ilorin na jihar Kwara
- Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa ɗan Achaɓan sai da ya shafe sa'o'i uku a ƙasan tirelar kafin a ciro shi
- Hukumomi sun ɗora alhakin aukuwar hatsarin akan gudun gangancin da ɗan Achaɓan da yake yi
Jihar Kwara - Wani ɗan Achaɓa ya rasa ransa a wani hatsarin da ya ritsa da motar tirela a birnin Ilorin, babban birnin jihar Kwara.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa lamarin ya auku ne akan titin hanyar Maraba-Zango cikin birni Ilorin da misalin ƙarfe 2:00 na rana a ranar Asabar, 9 ga watan Satumba.
Wani shaidar ganau ba jiyau ba wanda ba ya son a bayyana sunan shi, ya bayyana cewa mamacin ya shafe kusan sa'o'i uku a ƙasan tirelar kafin a ciro shi.
"Mamacin ya shafe kusan sa'o'i uku maƙale a ƙasan tirelar kafin a samu nasarar ciro shi, yayin da sauran mutum biyu da hatsarin ya ritsa da su, wata mata da wata ƙaramar yarinya aka garzaya da su zuwa asibiti." A cewarsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumomi sun tabbatar da aukuwar lamarin
Da yake magana kan lamarin, Kwamandan hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC) na jihar Kwara, Frederick Ade Ogidan, ya ɗora alhakin aukuwar hatsarin akan gangancin ɗan Achaɓan.
Ya bayyana cewa hatsarin ya auku ne lokacin da direban tirelar ya yi ƙoƙarin kaucewa ɗan Achaɓan wanda ya shigo hannunsa da gudun tsiya, rahoton Daily Post ya tabbatar.
Tun da farko wasu bayanai sun yi iƙirarin cewa dukkanin mutane ukun da ke kan babur ɗin ne suka rasu a hatsarin.
Amma Ogidan ya bayyana cewa
"Ɗan Achaɓan ne kawai ya rasu a hatsarin, yayin da sauran mutum biyun aka kai su asibitin koyarwa na jami'ar Ilorin (UITH)."
Jirgin Ruwa Ya Yi Hatsari a Neja
A wani labarin na daban, wani jirgin ruwa ɗauke da manoma masu yawa ya yi hatsari a yankin Mokwa na jihar Neja.
Jirgin ruwan ya kife ne lokacin da yake tafiya da manoman zuwa Tundun-Mangu daga ƙauyen Gbajibo a ƙaramar hukumar Mokwa ta jihar.
Asali: Legit.ng