Mutane 15 Sun Mutu Yayin da Jirgin Ruwa Ya Nutse a Jihar Adamawa
- Jirgin ruwa ya nutse da mutane sama da 20, ana fargabar mutum 15 daga cikin sun kwanta dama a jihar Adamawa
- Wani ganau ya ce lamarin ya faru ne yayin da wata iska mai ƙarfi ta riƙa tunkuɗo ruwa yana shiga cikin jirgin da yammacin ranar Jumu'a
- Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar ya ce har yanzun ba a ciro ragowar mutane 15 ba
Jihar Adamawa - Rahotanni sun bayyana cewa aƙalla mutane 15 suka mutu yayin da wani jirgin ruwa da ya ɗauko Fasinjoji harda kananan yara ya yi hatsari a jihar Adamawa.
Daily Trust ta ruwaito cewa hatsarin ya faru ne lokacin da Jigin Kwale-Kwalen, wanda ya ɗauko 'yan kasuwa, kananan yara da manoma ya taso daga ƙauyen zuwa Yola.
An ce jirgin ruwan ya kife ne a tafkin Njuwa kusa da ƙauyen Dandu, ƙaramar hukumar Yola ta Kudu a jihar Adamawa da yammacin ranar Jumu'a.
Wani ma'aikacin ba da agajin gaggawa na Red Cross, wanda ya zanta da wakilan jaridar ta wayar salula daga wurin da hatsarin ya auku, ya ce a yanzu sun tsamo gawar mutane huɗu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Majiyoyi sun bayyana cewa masu aikin jin ƙai da masu kawo ɗauki sun matsa kaimi wajen laluben ragowar mutanen da suka nutse, Sahara Reporters ta rahoto.
Wani shaidan gani da ido, Faisal Dabo, wanda ya zanta da ‘yan jarida ya ce guguwar iska mai karfi ce ta riƙa tunkuɗa ruwa cikin Kwale-Kwalen, kwatsam ya kife.
Ya yi kira ga hukumomi da su samar da jiragen ruwa na zamani masu injina ga al’ummar Rugange da ke fama da matsalar ambaliyar ruwa a kogin Benue duk shekara.
Za a ci gab aikin ceto yau Asabar
Da yake tabbatar da lamarin, Sakataren hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Adamawa (ADSEMA), Dakta Muhammad Amin Sulaiman, ya ce an ceto mutane 7, an tabbatar da mutuwar 2 yayin da 15 suka bace.
Ya yi kira da a kwantar da hankula yayin da hukumomi ke kokarin gano fasinjojin da suka bace, yana mai cewa za a ci gaba da binciken da karfe 10 na safiyar ranar Asabar.
Jihar Edo: Wani Magidanci Ya Halaka Matarsa Kan Sabanin Abinci
A wani labarin na daban kuma 'Yan sanda sun kama wani magidanci ɗan shekara 21 bisa zargin kashe matarsa kan saɓanin abinci a jihar Edo.
Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar 'yan sanda reshen jihar Edo, SP Chidi Nwanbuzor, ya ce an kama Magidancin ne ranar 30 ga watan Agusta, 2023 ta hannun caji ofis ɗin Fugar.
Asali: Legit.ng