Gwamnatin Tinubu Zata Gina Gidaje 7,000 a Wasu Jihohin Arewacin Najeriya

Gwamnatin Tinubu Zata Gina Gidaje 7,000 a Wasu Jihohin Arewacin Najeriya

  • Gwamnatin Bola Tinubu za ta gina gidaje 1000 a kowace jiha daga cikin jihohi 7 da rashin tsaro ya addaba a arewacin Najeriya
  • Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya ce shugaba Tinubu ya ware makudan kudaɗe don warware matsalar 'yan arewa
  • Ya kuma bayyana cewa kowane ɓangare a ƙasar nan zai amfana da kudirin shugaba Tinubu na kawo ci gaba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Gwamnatin tarayya zata gina gidaje. 7,000 a jihar Kaduna da sauran jihohin da matsalar tsaro ta shafa a arewacin Najeriya.

Channels tv ta rahoto cewa gwamnatin zata gina gidajen bayan shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da lamarin.

Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima.
Gwamnatin Tinubu Zata Gina Gidaje 7,000 a Wasu Jihohin Arewacin Najeriya
Asali: UGC

Baya ga jihar Kaduna, sauran jihohin da za a gina sabbin gidajen sun haɗa da Kebbi, Sakkwato, Katsina, Zamfara, Neja da kuma jihar Benuwai.

Kara karanta wannan

Tinubu: Gwamnan PDP Ya Manna Hotonsa a Jikin Buhunan Shinkafa, Ya Faɗi Dalili

Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ne ya bayyana haka ranar Jumu'a a Maiduguri, babban birnin jihar Borno yayin kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin jihar ta yi cikin kwanaki 100.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tinubu ya ware N50bn ga Arewa maso Yamma

Shettima, tsohon gwamnan Borno, wanda ya wakilci shugaba Tinubu a wurin kaddamar da ayyukan, ya ce Tinubu ya ware wa tsarin Paluku Naira biliyan 50.

A cewarsa, Tinubu ya amince da bai wa hukumar bada agajin gaggawa (NEMA) kuɗin N50bn domin fara aiwatar da tsarin da nufin waware matsalolin da suka addabi mutanen Arewa maso Yamma.

A wata sanawa da ta fito daga hadiminsa, Olusola Abiola, Shettima ya ce:

"Shugaban kasa ya amince da gina gidaje 1000 a jihohin Sokoto, Kebbi, Katsina, Zamfara, Kaduna, Neja da Benuwai tare da sauran kayayyakin more rayuwa na makarantu, Asibitoci da wuraren kiwon dabbobi ga Fulani."

Kara karanta wannan

"Ɗalibi Mai Hazaƙa" Daga Ƙarshe, Shugaba Tinubu Ya Bayyana Gaskiyar Tarihin Karatunsa a Jami'a

Shettima ya ce duka sassan kasar nan za su ci gajiyar ci gaban da shugaba Tinubu yake shirin kawo wa, yayin da ya kuma bayyana shirin gwamnatin tarayya na sake farfado da noman alkama.

Ya kara da cewa shugaba Tinubu na sane da kalubalen da ‘yan Najeriya ke fuskanta kuma zai yi duk kokarin da ya kamata wajen magance su, rahoton Vanguard ya tabbatar.

Sarkin Ningi Ya Yi Barazanar Tsige Sarakunan Da Ke Taimakon Yan Bindiga

A wani rahoton na daban Sarkin Ningi ya yi barazanar tsige duk hakimi ko mai Anguwan da ya kama da hannu a ayyukan bara gurbin yan bindiga.

Alhaji Yunusa Muhammadu Danyaya, ya ce rahoton da masarautarsa ta samu ya nuna akwai haɗin bakin wasu masu unguwanni a matsalar tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262