Jami'an 'Yan Sanda A Kano Sun Haramta Hawan Angonci Da Taron Majalisi Saboda Tsaro

Jami'an 'Yan Sanda A Kano Sun Haramta Hawan Angonci Da Taron Majalisi Saboda Tsaro

  • A kokarin rage tayar da tarzoma a birnin Kano, jami'an tsaro sun haramta hawan angonci a jihar
  • Har ila yau, 'yan sanda sun haramta taron majlisi da ake yi don dakile tare da rage matsalolin tsaro
  • Wannan na zuwa ne bayan bata-gari na amfani da wannan dama don aikata laifuka da sace-sace

Jihar Kano - Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta haramta kilisa da hawan angonci da taron majlisi ba tare da izini ba a fadin jihar.

Kakakin rundunar a jihar, Abdullahi Kiyawa shi ya bayyana haka inda ya ce kwamishinan 'yan sanda, Mohammed Usaini Gumel ne ya ba da umarnin hakan.

'Yan sanda a Kano sun haramta hawan angonci da kilisa
Rundunar 'Yan Sanda A Kano Sun Haramta Hawan Angonci Da Kilisa. Hoto: Kano Police.
Asali: Facebook

Meye dalilin matakin a Kano?

Ya ce an dauki matakin ne ganin yadda tabarbarewar tsaro ke kara yawa musamman a birnin Kano.

Kara karanta wannan

Hawaye Sun Kwaranya Yayin Da Matashi Ya Farmaki Malamin Addinini Tare Da Ajalinsa Da Adda, An Bazama Nemanshi

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wannan mataki na zuwa ne bayan wasu bata-gari na amfani da wuraren don aikata munanan laifuka don biyan bukatar kansu, TRT Hausa ta tattaro.

Gunel ya ce:

“Mun lura cewa matasa na karya doka tare da amfani da irin wannan lokaci don aikata manyan laifuka."
“Bincike ya nuna cewa hawan kilisa da hawan angonci da taron majalisi su ne wuraren da ake samun matsala tsakanin matasa."

Kwamishinan ya tabbatar cewa a baya hukumomi sun taba saka irin wadannan dokoki sai dai ba a samu abin da ake bukata ba dalilin dokar, cewar FRCN.

Meye 'yan sanda ke cewa a Kano?

Ya kara da cewa:

"A yau 7 ga watan Satumba mun yi taro da 'yan majalisar Sarki kan hawan dawaki, mun zartar da hukunci kan haramcin hawan angonci ko kilisa ko kuma taron majalisi dole a bi ka'ida na neman izini.

Kara karanta wannan

Tinubu: Gwamnan PDP Ya Manna Hotonsa a Jikin Buhunan Shinkafa, Ya Faɗi Dalili

“Saboda gudun kar bata-gari su shiga cikinsu su yi amfani da damar wadannan tarukan su aikata wani abu na cutar da al’umma,”

Gumel ya ce jami'ansu za su saka ido don tabbatar da bin dokar tare da kama wadanda su ka saba dokar.

Ya kara da cewa idan su ka bi ka'idojin dole su yi shiga mai kyau ba tare da saka guntun wando ba ko kuma rashin saka hula wannan saba ka'aida ne.

'Yan Sanda Sun Cafke Dan Daba A Kano

A wani labarin, jami'an 'yan sanda a jihar Kano sun cafke daya daga cikin 'yan daba da ake nema ruwa a jallo.

An kama matashin ne mai suna Sadiq da aka fi sani da 'Big Star' yayin da ya ji wa wani dattijo rauni da almakashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.