Annoba Ta Aukawa Abuja, Mutane Da-Dama Sun Sheka Barzahu a Birnin Tarayya

Annoba Ta Aukawa Abuja, Mutane Da-Dama Sun Sheka Barzahu a Birnin Tarayya

  • Bayin Allah sun rasu a sanadiyyar zaizayewar da kasa ta yi wajen satar ma’adanai a birnin Abuja
  • Mutum 50ne su ka mutu a sakamakon annobar da kuma garkuwa da mutane da ‘yan bindiga su ka yi
  • A matsayin ministan Abuja, Nyesom Wike ya yi alkawarin hada-kai da hukumomi domin kawo tsaro

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Mutane akalla 30 aka tabbatar da mutuwarsu a sakamakon ruftawar da kasa tayi a babban birnin tarayya watau Abuja.

Vanguard da ta fitar da labarin dazu, ta bayyana cewa masu bin barauniyar hanya wajen hako ma’adanai su ka jawo annobar.

Wannan lamari mara dadi ya auku ne a yankin karamar hukumar Kuje a birnin na Abuja.

Wike.
Ministan birnin Abuja, Nyesom Wike Hoto: @Topboychriss
Asali: Twitter

Baya ga haka kuma an samu labarin satar mutane 19 da aka yi a karamar hukumar Bwari, wannan ya jawo za a karfafa tsaro.

Kara karanta wannan

SSS Ta Cafke ‘Yan Uwan Tsohon Shugaban Hukumar EFCC Abdulrasheed Bawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An samu wadannan bayanai ne yayin da shugabannin kananan hukumomin Abuja su ka zauna da Ministan birni, Nyesom Wike.

Nyesom Wike wanda ya girgiza da jin labarin duk abin da ya faru, ya yi alkawarin zama da shugabannin hukumomin tsaro.

An rahoto Ministan ya na cewa zai hadu da Darektan jami’an DSS da Kwamishinan ‘yan sanda domin ceto wadanda aka sace.

Ministan Abuja zai hadu da Dele Alake

Mai girma Ministan ya kuma umarci shugabannin kananan hukumomin su kafa dakaru da za su lura da masu hako ma’adanai.

Har ila yau, Leadership ta ce tsohon gwamnan ya yi alkawarn haduwa da Dele Alake wanda shi ne ministan ma’adanai na tarayya.

Ana sa rai idan ministocin sun zauna, a iya fito da dabarun da za a bi wajen kawo karshen masu satar ma’adanai a birnin tarayyar.

Kara karanta wannan

Hannatu Musawa da Ministoci 4 da Su ka Jawo Rudani a Cikin Kwana 15 a Ofis

Ana neman taimakon Ministan birnin Abuja

Shugaban hukumar Bwari, Danladi Chiya ya jerowa Wike irin matsalolin da su ke fuskanta, ya na mai rokon ministan ya agaza masu.

Haka abin yake da Abdullahi Sabo wanda shi ne shugaban karamar hukumar Kuje, ya ce masu hakar ma’adanan sata sun hana su sakat.

Za ayi ruwa kamar da bakin kwarya

Dazu aka samu rahoto cewa NiMet ta ce awa 24 za a shafe ana ruwa mai tafe da iska da walkiya har da kuma ambaliya kwanan nan.

Masana sun yi hasashe cewa Riba, Delta, Jigawa, Katsina da Kano su na cikin inda za a iya fuskantar ambaliya a ranar Asabar dinnan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng