Gwamnatin Abba Gida Gida Na Shirin Rusa Gadar Gwarzo? Gaskiya Ta Bayyana
- Gwamnatin Abba Gida Gida ta yi watsi da rade-radin cewa tana shirin rusa gadar Gwarzo da ke jihar Kano
- Kwamishinan labarai na jihar, Malam Halilu Dantiye, ya ce gwamnatin Kano ta tura tawagar injiniyoyi domin su duba gadar don aiki a kanta
- Al'ummar yankin Gwarzo dai sun gudanar da zanga-zanga bayan samun labarin cewa gwamnati na shirin rusa gadar da Sanata Jibrin ya sake ginawa
Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa bata shirin rusa wata gada a garin Gwarzo, hedkwatar karamar hukumar Gwarzo.
An tattaro cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ne ya gina gadar.
Gwamnatin Abba gida gida ta tura injiniyoyi don su duba aikin gadar Gwarzo
Kwamishinan labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, Malam Halilu Dantiye ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a garin Kano a ranar Laraba, 6 ga watan Satumba, Daily Trust ta rahoto.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya ce wasu mutane sun tunkari gwamnatin jihar karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida Gida suna masu neman a sake gina gadar wacce ta rushe.
A cewarsa, tuni gwamnati ta tattara tawagar injiniyoyinta da suka duba gadar da abin ya shafa, ya kara da cewa ana ci gaba da gudanar da aikin da ya kamata a gadar.
Dantiye ya kuma ce gwamnatin na jiran samun rahotannin gina gadar ta hanyar da ta dace.
Al'ummar Gwarzo sun fusata kan rade-radin rusa gadar yankin
Tun farko dai, jaridar The Guardian ta rahoto cewa hankula sun tashi a karamar hukumar Gwarzo ta jihar Kano bayan rade-radin cewa gwamnati na shirin rusa gadar da Sanata Barau ya sake ginawa.
Hakan ya fusata al'umma inda mazauna garin Gwarzo da ke yankin Kano ta arewa suna gudanar da zanga-zanga don nuna rashin amincewarsu kan wannan yunkuri da gwamnatin ke yi.
An tattaro cewa gadar ta rushe ne kimanin mako uku da suka gabata sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a yankin.
Biyo bayan tsaiko da aka samu a wajen zirga-zirgar ababen hawa, mazauna yankin sun nemi gwamnatin jihar ta sa baki domin gyara ta, amma abin ya ci tura.
Amma daga karshe sai aka sami taimako a lokacin da Sanata Jibrin ya umarci wani dan kwangila ya gyara gadar.
Ba a bi tsari wajen sake gina gadar ba, Kwamishinan ayyuka na jihar Kano
Sai dai kuma, kwamishinan ayyuka na jihar, Marwan Ahmad, ya bayyana cewa ba a bi tsarin da ya kamata ba wajen sake gina gadar.
Ya soki tsoma bakin da Jibrin ya yi a lokacin da gwamnati ke kammala shirye-shiryen sake gina gadar.
A cewar kwamishinan, Sanata Jibrin (Kano ta Arewa) bai nemi izini da amincewar gwamnatin jihar ba kafin ya fara aikin.
Ya dage cewa Sanatan ba shi da hurumin gudanar da aikin gina hanyar gwamnatin jihar.
Nadin Mukamai: Abba Gida Gida Ya Jawo Matasa 44, Ya Sakala a Ma’aikatun Kano
A wani labarin, mun ji cewa Abba Kabir Yusuf ya dauko matasa ya ba su wani mukami da aka kira SSR da SR watau masu tattara rahotanni na musamman daga MDAs.
Malam Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar da sanarwa a shafinsa a matsayinsa na babban sakataren yada labaran Mai girma gwamnan Kano.
Asali: Legit.ng