Kotun Zabe Ta Tabbatar Da Nasarar Abdulmumini Jibrin a Matsayin Dan Majalisar Tarayya

Kotun Zabe Ta Tabbatar Da Nasarar Abdulmumini Jibrin a Matsayin Dan Majalisar Tarayya

  • Kotun zabe ta tabbatar da nasarar Abdulmumi Jibrin a matsayin dan majalisar tarayya mai wakiltan mazabar Bebeji/Kiru ta jihar Kano
  • Mai shari'a Ngozi Flora ta yi watsi da karar da dan takarar APC, Muhammad Sa'id Kiru ya shigar kan nasarar Kofa
  • Saboda bata mata lokaci da ya yi wajen sauraron shari'ar wacce ta ce ba ta da inganci, kotun ta ci tarar Kiru kan kudi naira 100,000

Jihar Kano - Kotun sauraron kararrakin zaben yan majalisar tarayya da ke zama a Kano ta yanke hukunci cewa Muhammad Sa'id Kiru na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya gaza gabatar da shaidu da za su tabbatar da an tauye masa hakki a yayin zaben 2023.

Kotun zaben ta yi watsi da karar da ya shigar kan nasarar Abdulmumini Jibrin Kofa na jam'iyyar NNPP a ranar Laraba, 6 ga watan Satumba, Solacebace ta rahoto.

Kara karanta wannan

Jigon APC Ya Yi Garaje, Ya Fadi Wanda Zai Yi Nasara a Kotun Karar Zaben 2023

Kotu ta tabbatar da nasarar Abdulmumin Jibrin a Kano
Kotun Zabe Ta Tabbatar Da Nasarar Abdulmumini Jibrin a Matsayin Dan Majalisar Tarayya Hoto: Abdulmumin Jibrin
Asali: Facebook

Abdulmumin Jibrin ne zababben dan majalisar tarayya mai wakiltan mazabar Bebeji da Kiru, kotu

Kwamitin alkalan mai mutum uku karkashin jagorancin, Mai Shari’a Ngozi Flora, ya ce takardun da bangarorin biyu suka gabatar a gaban kotun sun nuna Jibrin Kofa ya yi murabus daga kujerarsa na babban sakataren hukumar gidajen tarayya kwanaki 30 kafin zaben 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kotun zaben ta bayyana cewa wanda yake karar ya gaza cika hujjoji da za su tabbatar da cewar an tafka magudi a zaben ba tare da bin tanadin dokar zaben 2022 kamar yadda aka gyara.

Da take yanke hukunci, mai shari'ar ta ce an yi watsi da karar saboda rashin cancanta tare da tabbatar da Jibrin Kofa a matsayin zababben dan majalisar tarayya mai wakiltan mazabar Bebeji da Kiru daga jihar Kano.'

Har ika yau, kotun ta kuma ci tarar wanda ya shigar da karar kudi 100,000 saboda bata mata lokaci, rahoton Aminiya.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar NNPP Ta Doke Abba Ganduje a Kotu a Karar Zaben ‘Dan Majalisa a Kano

An kori Rabiu Kwankwaso daga jam'iyyar NNPP

A wani labari na daban, mun ji cewa an kori dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Sanata Rabiu Kwankaso, daga jam’iyyar.

Kamar yadda jarida The Nation ta rahoto, kwamitin zartarwar jam’iyyar na kasa (NEC) ne ya sanar da batun korar Sanata Kwankwaso.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng