Yajin Aikin NLC Ya Kawo Tsaiko a Yanke Hukuncin Kotun Zabe a Jihar Ogun
- An samu jinkiri a zaman Kotun sauraron kararrakin zaben 'yan majalisar tarayya mai zama a Kotun sakamakon yajin aikin NLC
- Ma'aikatan shari'a sun garƙame Kofar shiga Ƙotun wacce ta shirya yanke hukunci kan zaben Sanatan Ogun ta yamma ranar Laraba
- Hakan ya dakatar da zaman Kotun kuma a cewar shugaban JUSUN sun kulle ƙofar ne bisa umarnin NLC ta ƙasa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Ogun - Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an samu tsaiko a shirin yanke hukunci a Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen 'yan majalisun tarayya mai zama a Abeokuta, jihar Ogun.
Zaman Kotun na yau Laraba ya samu jinkiri yayin da ma'aikatan shari'a suka garƙame kofar shiga harabar Kotun sakamakon yajin aikin ƙungiyar kwadago NLC.
Shugabannin ƙungiyar ma'aikatan shari'a ta Najeriya (JUSUN) ne suka kulle kofar shiga Kotun Majistire mai zama a Isabo, Abeokuta, wurin da Kotun sauraron ƙarar zaɓen ke zama.
An tattaro cewa sun yi haka ne domin biyayya ga matakin ƙungiyar kwadago ta ƙasa (NLC) na shiga yajin aikin gargaɗi na kwanaki biyu wanda aka fara ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yajin aikin gargaɗin NLC da sauran ƙawayenta na nuna adawa da tuge tallafin man Fetur ya fara daga jiya Talata kuma ana tsammanin za a ƙarƙare shi daga lokacin tashi aiki yau Laraba.
Wane hukunci Ƙotun zata yanke yau Laraba?
Bayanai sun nuna cewa Kotun zaɓen NASS ta zaɓi yau Laraba, 6 ga watan Satumba domin yanke hukunci kan ƙarar da aka shigar da Sanata mai wakiltar Ogun ta yamma, Solomon Olamilekan Adeola.
Ɗan takarar Sanata a mazaɓar karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Dada Ganiyu Adeleke, shi ne ya shigar da ƙarar mai lamba EPT/OG/Sen/2023, Premium Times ta rahoto.
Meyasa ma'aikata suka garkame Kotun?
Tashin Hankali Yayin Da Tsaffin Tsagerun Neja Delta Suka Dira Kotun Zaben Shugaban Kasa, Bayanai Sun Fito
Shugaban JUSUN na jihar, Kwamared Olanrewaju Ajiboye ya ce ma’aikatan shari’a sun kulle kofar ne domin bin umarnin ƙungiyar ta kasa kan yajin aikin gargadi na kwanaki biyu.
Ya ce:
“A yau ne ake sa ran kotun za ta zauna, amma su (alkalai) ba su samu damar zama ba saboda mun kulle kofar Kotun bisa bin umarnin kungiyar NLC ta kasa. Wannan shine dalilin da ya sa Kotun ta kasa zama a yau."
Shugaba Tinubu Ya Sauka a Indiya, Ya Gana da Fitaccen Attajirin Ƙasar
A wani labarin na daban Bola Ahmed Tinubu ya isa ƙasar Indiya domin halartar taron G20, ya gana da shugaban rukunin kamfanonin Hinduja Group.
Shugaban ƙasar ya ce ƙofar Najeriya a buɗe take wajen zuba hannun jari wanda zai samar da ayyukan yi a karkashin gwamnatinsa.
Asali: Legit.ng