Yan Sanda Sun Cafke Masu Garkuwa Da Mutane 32 a Jihar Adamawa

Yan Sanda Sun Cafke Masu Garkuwa Da Mutane 32 a Jihar Adamawa

  • Rundunar ƴan sandan jihar Adamawa ta samu nasarar cafke miyagun masu garkuwa da mutane a jihar
  • Rundunar ƴan sandan ta sanar da cewa ta cafke masu garkuwa da mutane da fashi da makami mutum 32
  • Kwamishinan ƴan sandan jihar ya karrama jami'an yan sanda da mafarautan da suka taimaka wajen cafke miyagun masu laifin

Jihar Adamawa - Rundunar ƴan sandan jihar Adamawa ta cafke masu garkuwa da mutane da fashi da makami mutum 32 a jihar.

Rundunar ƴan sandan ta kuma ƙwato motoci huɗu da tsabar kuɗi har N1.6m daga hannun waɗanda ake zargin, rahoton Leadership ya tabbatar.

Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane a Adamawa
Mukaddashin babban sufetan yan sanda na kasa, Kayode Adegbotekun Hoto: @NigeriaPoliceForce
Asali: Facebook

Daga cikin waɗanda ake zargin da aka cafke waɗanda aka tasa ƙeyarsu a jiya Litinin, 4 ga watan Satumba, akwai wani Mustapha Mohammed, wanda ake zargi da sace Zainab Abbas, matar alƙalin babbar kotun Adamawa.

Kara karanta wannan

Hukumar DSS Ta Kama Jami'an Gwamnati Da Ke Karkatar da Tallafin da Ake Raba Wa Talakawa

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje, a cikin wata sanarwa shi ne ya tabbatar da cafke waɗanda ake zargin, rahoton The Nation ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nguroje ya bayyana cewa daga cikin abubuwan da aka ƙwato a hannun waɗanda ake zargin sun haɗa da bindigu ƙirar AK-47 guda 13, ƙananan bindigu guda biyar, harsasai 59 na bindiga ƙirar AK48 masu kaurin 7.62mm, harsasai 72 masu kaurin 0.6mm manyan bindigu guda huɗu.

An karrama jami'an ƴan sandan da suka cafke su

Kwamishinan ƴan sandan jihar, Afolabi Babatola, bayan kammala tasa ƙeyar masu garkuwa da mutanen, ya miƙa lambobin yabo ga jami'an ƴan sanda 11 da mafarauta waɗanda suka taimaka wajen cafke miyagun.

Daga cikin waɗanda aka karrama akwai, shugaban tawagar Crack Squad, SP Hussaini, DSP Martina Panchiri, ASP Dahiru Tajudeen, ASP Salman Adamu, Insfeta Ibrahim Musa da wasu mafarauta.

Kara karanta wannan

Nasara: 'Yan Sanda Sun Ceto Mutane 3 da Aka Sace a Zaria, Sun Tona Asirin Masu Hannu a Harin

Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 2 a Kaduna

A wani labarin na daban kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun kai mummunan harin ta'addanci a garin Jere na ƙaramar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna.

Miyagun ƴan bindiga waɗanda suka yo gayya kan babura ɗauke da miyagun bindigu, sun halaka mutum biyu, tare da sace wasu mutum 11 waɗanda ke aiki a wani gidan biredi da ke garin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng