Bulama Bukarti Ya Bayyana Dalilin Da Zai Hana Kotu Yanke Hukunci a Ranar Laraba

Bulama Bukarti Ya Bayyana Dalilin Da Zai Hana Kotu Yanke Hukunci a Ranar Laraba

  • Wani sanannen lauya, Bulama Bukarti ya bayyana cewa kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ba lallai ba ne ta yanke hukuncinta a ranar Laraba
  • Ya bayyana cewa yajin aikin ƙungiyar ƙwadago ka iya hana alƙalan samun shiga harabar kotun da ofisoshinsu
  • Sai dai, Bukarti, ya bayyana cewa kotun ka iya ɗage sanar da hukuncinta har sai bayan an kammala yajin aikin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani sanannen lauya ɗan Najeriya, Bulama Bukarti, ya bayyana dalilin da zai sanya kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa (PEPT), ta kasa yanke hukuncinta a ranar Laraba, 6 ga watan Satumba.

Bukarti ya bayyana cewa akwai yiwuwar yajin aikin da ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC), ke yi na iya hana kotun yanke hukuncinta.

Bulama ya ce yajin aiki zai hana kotu yanke hukunci
Bulama ya yi magana kan yiwuwar yajin aiki ya hana kotun zaben shugaban kasa yanke hukunci Hoto: @bulamabukarti
Asali: Twitter

Yaji aikin NLC ka iya hana kotu yanke hukunci

A wani rubutu da ya yi a shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) @bulamabukarti, ya yi nuni da cewar ƙungiyar ma'aikatan sharia ta Najeriya (JUSUN), ta bayar da umarnin rufe dukkanin kotuna a ranakun Talata 6 ga wata da Laraba, 6 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Atiku, Obi Da Tinubu: Jigon PDP Ya Ce Bai Dace Kotu Ta Ayyana Wanda Ya Yi Nasara Ba, Ya Fadi Abinda Ya Kamata a Yi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya cigaba da cewa kulle harabar kotun da ofisoshin alƙalan, kai tsaye zai hana alƙalan yanke hukuncinsu.

A kalamansa:

"Sai dai, kotun ka iya dakatar da yanke hukuncin har sai yajin aikin ya ƙare, zuwa can da yamma ko farkon dare. Amma hakan ba lallai ya yiwu ba saboda JUSUN ka iya ƙin buɗe kotun bayan lokacin aiki ya ƙare ko jami'an NLC su kulleta har sai safiyar ranar Alhamis. Na ƙosa domin ganin abin da zai faru gobe."

Yajin aikin gargaɗi na kwana biyu da ƙungigar ƙwagadon ke yi, ya dakatar da abubuwa sosai a ƙasa inda abubuwa suka tsaya cak.

Ƙungiyar ta fara yajin aikin gargaɗin ne kwana biyu domin nuna adawa da cire tallafin man fetur sa gwamnatin tarayya ta yi.

Yajin Aiki Ya Jawo An Dambace

A wani labarin kuma, jami'an ƙungiyar ƙwadago (NLC) a jihar Ondo sun ba hammata iska da wasu ma'aikata kan yajin aikin gargaɗi na kwana biyu.

Kara karanta wannan

Shari'ar Atiku, Obi Da Tinubu: Jami'an Tsaro Sun Fitar Da Muhimmin Gargaɗi Gabanin Yanke Hukunci

Jami'an na NLC dai na ƙoƙarin tabbatar da bin umarnin yajin aikin gargaɗin ne lokacin da suka hammata iska da ma'aikatan da suka fita ofisoshinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng