NYSC Ta Bayyana Lokacin Da Yakamata Masu Hidimar Kasa Su Rika Tafiya
- Hukumar kula da masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) ta bayyana cewa ta gargaɗi masu yi wa ƙasa hidima kan yin tafiyar dare
- Eddy Megwa, darektan watsa labarai na hukumar ya bayyana cewa da masu yi wa ƙasa hidima na kiyaye hakan da ba a riƙa sace su ba
- Megwa ya yi bayanin cewa hukumar ta daɗe tana wayar da kan masu yi wa ƙasa hidima kiyaye yin tafiyar dare saboda rashin tsaro
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Hukumar kula da masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) ta bayyana cewa ta shawarci masu yi wa ƙasa hidima, su daina yin tafiya da daddare.
Eddy Megwa, darektan watsa labarai na hukumar NYSC, shi ne ya bayyana hakan a yayin wata tattaunawa da gidan talbijin na Channels tv.
Megwa yana magana ne bayan ƴan bindiga sun sace wasu masu yi wa ƙasa hidima mutum takwas, a kan titin zuwa jihar Zamfara a ranar 19 ga watan Agusta.
Masu yi wa ƙasa hidimar dai sun taso ne daga birnin Uyo na jihar Akwa Ibom inda suka biyo ta Sokoto domin zuwa jihar Zamfara yin aikin hidimtawa ƙasa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ba su ɗauki shawara ba
Ya bayyana cewa da ace masu yin hidimar ƙasar sun kiyaye gargaɗin hukumar na kada su yi tafiya bayan ƙarfe 6:00 na yamma, da ba a sace su ba.
Sai dai, Megwa ya bayyana cewa hukumar tana iya bakin ƙoƙarinta domin tabbatar da cewa an sako su cikin ƙoshin lafiya.
NYSC ta shawarci masu yi wa ƙasa hidima
Ya kuma buƙaci masu yi wa ƙasa hidima da su kiyaye da matakan da hukumar ke ɗauka na kare lafiyarsu, ciki har da daina yin tafiya da daddare.
A kalamansa:
"Ka da mu kalli NYSC kamar tana wata duniya ne ta daban. NYSC tana cikin Najeriya. Da ni da kai duk mun san halin rashin tsaron da mu ke ciki a ƙasar nan, ba zaɓe ake yi ba, an sace wasu ɗalibai, an sace jami'an gwamnati, har ƙananan yara ƴan firamare an sace."
"Don haka NYSC ko masu yi wa ƙasa hidima ba a wata duniyar ta daban su ke rayuwa ba, amma mun yi gargaɗi. Mun gaya wa masu yi wa ƙasa hidima cewa ka da su yi tafiyar dare. A takardun kiransu zuwa hidimar ƙasa mun gaya musu hakan. Mun gaya musu cewa ko a ina su ke ƙarfe 6:00 na yamma na yi, su dakatar da tafiyarsu."
"NYSC na bakin ƙoƙarinta, ko kafin a fara buɗe sansanin horaswa, muna fitar da sanarwa a kafafen watsa labarai, mu gaya musu ka da su yi tafiyar dare. Hukumar ta yi dukkanin abin da yakamata ta yi."
An Shawarci NYSC Kan Tura Masu Yi Wa Kasa Hidima
A wani labarin kuma, an buƙaci hukumar masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) da ta daina tura masu hidimtawa ƙasa zuwa jihohin, Kebbi, Zamfara da Sokoto.
Tsohon shugaban kwamitin hukunta ƴan bindiga na jihar Zamfara, Sani Shinkafi, shi ne ya bayar da wannan shawarar, inda ya ce babu tsaro a waɗannan jihohin.
Asali: Legit.ng