“N330k Muka Siya”: Wani Mutum Ya Siya Motar Hannu, Kofar Ta Ki Budewa Bayan Ya Je Biki Da Ita

“N330k Muka Siya”: Wani Mutum Ya Siya Motar Hannu, Kofar Ta Ki Budewa Bayan Ya Je Biki Da Ita

  • Wani dan Najeriya ya siya wata tsohuwar mota kan N330k, amma motar ta dunga ba shi da iyalinsa ciwon kai
  • Matar mutumin ta bayyana halin da iyalin suka shiga sannan ta ce sun halarci wani biki da motar amma gaba daya kofofin suka ki budewa
  • Domin yi wa tufkar hanci, matar ta ce mijinta ya yanke shawarar mayar da motar ga wanda ya siyar masu da ita, amma ya ki karba

Wani dan Najeriya ya siya wata motar hannu kan kudi N330k don amfanin iyalinsa, amma sai abun ya zama ciwon kai.

Matar mutumin ta garzaya soshiyal midiya don bayyana yadda motar ta dunga kunyata su tun bayan da suka kai ta gida.

Wani mutum ya siya motar hannu, ta kai shi iyaka
An yi amfani da hotuna don misali ne kawai Hoto: Getty Images/Dan Reynolds Photography and Moyo Studio.
Asali: Getty Images

Da take ba da labarin abun da ya faru, matar ta bayyana cewa mijinta ya siya motar ne saboda mutanen gidansu na yanka da tasu motocin.

Kara karanta wannan

Kwanaki 100 Kan Mulki: Tarun Matsaloli 3 Da Ke Hana Shugaba Tinubu Sakewa Tun Bayan Hawanshi Mulki

Iyalin sun yanke shawarar shiga sahun masu mota don su fita daban a cikin makwabtansu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wata rana, sun tuka motar zuwa wajen wani biki, sai kofofin suka ki budewa yayin da suka isa wajen.

Ta ce:

"Motar abun kunya ce. Muna bukatar mayar da ita ga mutumin da muka siye ta a hannunsa. Mun ma ce za mu ba shi N50k amma ya ki. Na yau ya fi na kullun muni, mun shiga motar zuwa wajen wani biki, sai motar ta ki budewa."

Queen Precious Ose ce ta wallafa labarin a Facebook.

Martanin jama'a yayin da wani mutum ya mayar da motar da ya siya N330k mai wanda ya siyar masa

Queen Precious Ose ta ce:

"Kun siya 330k sannan kuna sa ran kofar ta dunga budewa."

Egharevba Kingsley ya ce:

Kara karanta wannan

Sanusi II Ya Yi Magana, Ya Haska ‘Barnar’ da Gwamnatin Buhari Tayi a Shekaru 8

"Ku siyar da sassan ta a matsayin kayan jari bola."

Mai hoto ya yanke kanwar amarya daga hotuna saboda ta hana shi abincin biki

A wani labari na daban, wani mai dauakr hoto ya bayyana rashin jin dadinsa a wani shagalin bikin aure da ya yi aiki.

A wani labari da ya yadu a soshiyal midiya, mai hoton ya ce kanwar amarya ce ta yi rabon abinci a wajen taron.

Ya ce lokacin da ya tambayeta abinci, sai matashiyar da ke rike da ragamar rabon abinci ta kunyata shi sosai. A cewarsa, ko ruwa ba a ba shi ya sha ba a bikin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng