"Ku Daina Tura Matasa Zuwa Jihohin, Sokoto, Kebbi da Zamfara" Shinkafi Ga NYSC
- Tsohon shugaban kwamitin hukunta masu aikata laifukan 'yan bindiga a Zamfara ya shawarci hukumar NYSC
- Sani Shinkafi ya yi kira ga NYSC ta daina tura matasa 'yan bautar ƙasa zuwa wasu jihohi da 'yan bindiga suka hana zaman lafiya
- Wannan kira na zuwa ne makonni kaɗan bayan sace wasu matasa 'yan bautar kasa a hanyarsu ta zuwa Zamfara
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Zamfara - Tsohon shugaban kwamitin hukunta 'yan bindiga a jihar Zamfara, Sani Shinkafi, ya roƙi hukumar kula da matasa 'yan bautar kasa (NYSC) ta daina tura matasa zuwa jihohin da babu zaman lafiya.
Shinkafi ya buƙaci NYSC ta dakatar da tura matasan masu hidima ga ƙasa zuwa jihohin da 'yan bindiga suka hana jama'a zaman lafiya a Arewacin Najeriya, Vanguard ta rahoto.
Ya lissafo wasu jihohi 3 a Arewa waɗanda yake ganin ya dace NYSC ta dakatar da tura matasa masu hidima ga ƙasa, jihohin su ne Zamfara, Kebbi da kuma Sakkwato.
Gaskiya Ta Fito: Obasanjo Ya Bayyana Abinda Ya Sa Ya Ɗauko Umaru 'Yar'adua Duk Ya San Ba Shi Da Lafiya
Wannan kalaman na Shinkafi na zuwa ne makonni ƙalilan bayan wasu miyagun 'yan bindiga sun yi garkuwa 'yan bautar kasa a babban titin Zamfara.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mista Shinkafi, wanda ya yi jawabi a Channels tv cikin shirinsu na safe 'Sunrise Daily' ya ce:
"Ina kira ga jagororin NYSC su dakatar da tura matasa masu bautar ƙasa zuwa jihohin Sakkwato, Kebbi da kuma Zamfara."
Shinkafi ya soki matakin gwamnatin Zamfara
Bugu da ƙari ya caccakin gwamnan Zamfara na yanzu, Dauda Lawal, bisa matakin da ya ɗauka na ƙin tattaunawar sulhu da tubabbun 'yan bindiga.
A cewarsa, matakin tsohuwar gwamnatin Bello Matawalle na tattaunawar neman sulhu da zaman lafiya da 'yan bindiga ya yi amfani wajen ceto mutanen da aka sace.
"Idan irin haka ta faru, muna kiran tubabbun 'yan bindiga su taimaka wa hukumomin tsaro wajen ceto mutane ko kuma su karɓo su ba tare da biyan kuɗin fansa ba."
"Amma daga zuwan wannan gwamnatin, an kashe mutane da yawa, wasu kuma an yi garkuwa da su. Mutanen da aka kashe da waɗanda aka yi garkuwa da su sun haura 2,000."
"Ba bu ƙaramar hukumar da ke zaune lafiya a jihar Zamfara."
Zan Bayyana Masu Hannu a Kashe-Kashen Rayuka Nan Da Mako Guda, Gwamna Uzodinma
A wani rahoton kuma Gwamna Uzodinma na jihar Imo ya lashi takobin bayyana masu ɗaukar nauyin kashe-kashen mutane a jiharsa.
Gwamnan ya jima yana nanata cewa wannan rashin tsaro da ƙaruwar ayyukan ta'addanci a jiharsa yana da alaƙa da siyasa.
Asali: Legit.ng