Kungiyar Yan Kasuwa Ta Fice Daga Yajin Aikin Kungiyar Kwadago Na Kwana 2, Ta Fadi Dalili

Kungiyar Yan Kasuwa Ta Fice Daga Yajin Aikin Kungiyar Kwadago Na Kwana 2, Ta Fadi Dalili

  • Duk da rokon da gwamnatin tarayya ta yi, kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta ce sai ta tafi yajin aikin da ta shirya
  • Sai dai wannan ci gaban ya hadu da gagarumin tangarda sakamakon sanarwar da reshenta, kungiyar yan kasuwa (TUC) ta yi
  • Bayan an kammala koma, TUC ta sanar da cewar ba da ita za a shiga yajin aikin kwana 2 da NLC ta kira ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kungiyar yan kasuwa ta TUC ta ce ba za ta shiga yajin aikin gargadi na gama gari da kungiyar kwadago ta shirya farawa a ranar Talata, 5 ga watan Satumba ba.

Kungiyar TUC ta zame jiki daga yajin aikin kungiyar kwadago
Kungiyar Yan Kasuwa Ta Fice Daga Yajin Aikin Kungiyar Kwadago Na Kwana 2, Ta Fadi Dalili Hoto: Daddy D.O @DOlusegun
Asali: Twitter

Shugaban kungiyar TUC, Kwamrad Festus Osifo ya bukaci kungiyar gwadagon da ta karfafa tattaunawa da gwamnati, tsarin da ta fara bi, PM News ta rahoto.

"Ya zuwa yau, bukatar shiga yajin aikin gama gari ba ta taso ba, don haka ya kamata shugabannin kungiyar su kara tattaunawa da gwamnati ta yadda za a shawo kan dukkan wuraren da ke da tangarda cikin wa'adin da aka bada," cewar Osifo bayan ganawa da ministan kwadago, Simon Lalong.

Kara karanta wannan

Bayan Cire Tallafin Fetur. Tinubu Ya Waiwayi Ma’aikata, Ya Koka Kan Albashin da Ake Biya

A makon jiya ne kungiyar NLC ta sanar da cewar mambobinta za su shiga yajin aikin gargadi daga ranar Talata.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Nan da mako uku masu zuwa, za ta shiga yajin aiki gaba daya don yin zanga-zanga kan tsadar rayuwa bayan gwamnati ta janye tallafin man fetur.

NLC ta shure tattaunawa da gwamnati

Tun farko dai mun ji cewa shugabannin kungiyar kwadago ta kasa (NLC) sun kaurace wa halartar taron da Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Simon Lalong, ya shirya a Abuja.

An tattaro cewa Ministan ya kira zaman ne da nufin shawo kansu su janye yajin aikin gargadi da suka shirya shiga a cikin makon nan.

Ganawar da aka shirya farawa da misalin karfe 3:00 na yammacin ranar Litinin, hakan ba ta samu ba sai ƙarfe 5:32 na yammaci sannan suka shiga taron, kamar yadda The Cable ta tattaro.

Kara karanta wannan

Shugabannin Ƙungiyar NLC Sun Kunyata Ministan Tinubu, Sun Fatali da Taron FG

Tinubu ya waiwayi ma’aikata, ya koka kan yawan wadanda ke cinye albashin gwamnati

A wani labarin kuma, mun ji cewa Bola Ahmed Tinubu ya nuna damuwarsa game da tulin ma’aikatan gwamnati da ake da su tun daga matakin jihohi zuwa tarayya.

Tribune ta ce Bola Ahmed Tinubu ya bayyana abin da yake cikin ran sa a lokacin da ya hadu da shugaban Oracle, Andres Garcia Arroyo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng