'Yan Nijar Sun Gaji da Hulda da Turawa, Sun Ce Dole a Fatattaki Sojojin Faransa a Kasar, Sun Yi Zanga-Zanga

'Yan Nijar Sun Gaji da Hulda da Turawa, Sun Ce Dole a Fatattaki Sojojin Faransa a Kasar, Sun Yi Zanga-Zanga

  • ‘Yan Nijar sun yi zanga-zangar neman ficewar sojin Faransa a kasar biyo bayan bukatar da sojin juyin mulkin kasar suka bayyana
  • Bayan juyin mulki, an samu kalamai da ke bayyana rashin aminci tsakanin sojin kasar da Faransa da ke da alaka ta kut-da-kut da Nijar
  • Baya ga Nijar, an yi juyin mulki a kasar Gabon bayan samun rashin daidaito a zaben da aka gudanar a kasar makon jiya

Yamai, Nijar - Dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a ranar Asabar a Yamai babban birnin jamhuriyar Nijar domin Faransa ta janye sojojinta kamar yadda rundunar sojin da ta kwace mulki a watan Yulin da ya gabata suka bukata.

Masu zanga-zangar dai sun taru ne a kusa da wani sansani na sojojin Faransa biyo bayan kiran da wasu kungiyoyin fararen hula da ke adawa da kasancewar sojojin Faransa a kasar suka yi.

Kara karanta wannan

Muje zuwa: Bayan rufe iyakan Gabon na kwanaki, shugaban soji ya fitar da sabuwar sanarwa

Zanga-zangar ta tumbatsa ne bayan bullowar dandazon jama’a a wurin da lamarin ya faru a birnin Yamai da ke jamhriyar ta Nijar, Channels Tv ta ruwaito.

'Yan Nijar sun nemi a kori Faransa
Lokacin da 'yan Nijar ke zanga-zanga | Hoto: France 24
Asali: Facebook

Alakar Nijar da Faransa na kara tsami

A ranar Juma'ar da ta gabata ne gwamnatin mulkin sojan Nijar ta yi wani sabon baut game da Faransa, inda ta zargi kasar da nuna "tsangwama a fili" ta hanyar mara wa hambararren shugaban kasar baya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A ranar 26 ga watan Yuli ne wasu jami'an tsaron fadar shugaban kasa suka tsare Shugaba Mohamed Bazoum biyo bayan hambarar da mulkinsa, Guardian ta tattaro.

Bazoum dai ya kasance shugaban Nijar da ya samu karbuwa a farko, inda ya yi yaki da masu tada kayar baya tare da wanzar da zaman lafiya a yankuna daban-daban na kasar.

Kara karanta wannan

"Juyin Mulkin Gabon Ya Faranta Min Rai Sosai", Fayose Ya Bayyana Dalili

Hambarar da Bazoum dai ya jawo cece-kuce a nahiyar Afrika, inda kungiyar ECOWAS ke bayyana Allah-wadai da yiwuwar daukar mataki kan lamarin.

Martanin AU ga juyin

A bangare guda, a ranar Laraba, shugaban Hukumar Tarayyar Afirka, Moussa Faki Mahamat, ya gargadi sojojin kasar Gabon da jami'an tsaro da su yi aikin da ya rataya a wuyansu na jamhuriyar.

Hakan dai na zuwa ne yayin da ya kuma yi kakkausar suka ga abin da ya bayyana a matsayin yunkurin juyin mulki a Gabon, Vanguard ta ruwaito.

Jami'an 'yan tawaye a kasar ta tsakiyar Afrika mai arzikin man fetur, sun sanar a safiyar Laraba cewa, sun kwace mulki, sakamakon kitmurmura a zabukan da aka takaddamar a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.