Bosun Jeje Tsohon Kwamishinan Gidaje Na Jihar Legas Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Bosun Jeje, tsohon kwamishinan gidaje na jihar Legas ya riga mu gidan gaskiya, kamar yadda babban yayansa, Fasto Adekunle Jeje ya tabbatar
- Jeje ya riƙe muƙamin kwamishinan gidaje a ƙarƙashin gwamnatin tsohon gwamna Babatunde Raji Fashola
- Sanata Gbenga Ashafa, tsohon sanatan Legas ta Gabas ya nuna kaɗuwarsa tare aike wa da saƙon ta'aziyyarsa kan rasuwar Jeje
Jihar Legas - Bosun Jeje, tsohon kwamishinan gidaje na jihar Legas, ya yi bankwana da duniya.
Babban yayan kwamishinan, fasto Adekunle Jeje, shi ne ya sanar da rasuwarsa a shafinsa na Facebook a ranar Asabar, 2 ga watan Satumban 2023.
"Allah ya yi maka rahama ƙanina Moshood Olatunbosun Adedeji Jeje wanda aka fi sani da BOJECO, Mr PARKERS ya rasu a ranar Asabar, 2 ga watan Satumban 2023. An yi jana'izarsa kamar yadda addinin musulunci ya tanada." A cewar sanarwar.
Legit.ng ta tattaro cewa Bosun Jeje ya riƙe muƙamin kwamishinan gidaje a lokacin gwamnatin tsohon gwamnan jihar Legas Babatunde Raji Fashola.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sanata Gbenga Ashafa ya yi ta'aziyyar Bosun Jeje
A halin da ake ciki, Sanata Gbenga Ashafa, tsohon sanatan Legas ta Gabas ya yi ta'aziyyar rasuwar Jeje, wacce ya bayyana a matsayin mai matuƙar kaɗuwa.
Sanatan a cikin wata sanarwa a shafinsa na Facebook ya rubuta cewa:
"Cikin kaɗuwa da baƙin ciki na rubuta domin aike wa da saƙon ta'aziyya ga dukkanin iyalan Jeje da shugabanni/mambobi na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Legas, musamman na mazaɓar sanatan Legas ta Gabas, bisa rasuwar Hon. Bosun Jeje da safiyar ranar Asabar, 2 ga watan Satumban 2023."
Ya bayyana marigayin a matsayin ɗan uwa, aboki, mutumin kirki, lauya, ma'aikacin banki, mai taimako, ɗan kasuwa kuma ɗan siyasa wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimtawa al'umma.
Muje Zuwa: Shehu Sani Ya Bayyana Jam'iyyar Da Za Ta Ci Ribar Rikicin Siyasar Da Ke Tsakanin Gwamnan PDP Da Mataimakinsa
Matar Tsohon Sanata Ta Rasu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sanatan Edo ta Arewa, Francis Alimikhena, ya yi babban rashi a rayuwarsa bayan matarsa ta riga mu gidan gaskiya.
Monica Francis Alimikhena ta yi bankwana da duniya ne a ranar Alhamis, 31 ga watan Agustan 2023.
Asali: Legit.ng