Shugaban APC Ganduje Ya Fadi Adadin Kuri’un da Yake So ’Yan Kogi Su Ba APC a Zabe Mai Zuwa
- Shugaban jam’iyyar APC, Ganduje a ranar Asabar, 2 ga watan Satumba, ya kaddamar da kwamitin kamfen a shirin zaben gwamnan jihar Kogi da za a gudanar a ranar 11 ga watan Nuwamba
- A yayin taron jam’iyyar, Ganduje ya bukaci mazauna Kogi da su zabi wanda zai gaji Gwamna Yahaya Bello, Alhaji Usman Ododo
- Tsohon gwamnan na Kano ya ci gaba da cewa jam’iyya mai mulki a jihar tana neman 99% na kuri’u da za a kada a rumfunan zabe
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kogi, Lokoja – Shugaban jam’iyyar APC mai mulki na kasa, Abdullahi Ganduje, ya dorawa al’ummar jihar Kogi alhakin ba jam’iyyar goyon baya da 99% na kuri’u a zaben gwamnan jihar da za a gudanar a ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba.
Kamar yadda jarida Punch ta ruwaito, Ganduje ya bayyana wadannan kalamai ne a ranar Asabar, 2 ga watan Satumba, yayin da yake jawabi ga mambobin jam’iyyar da magoya bayanta a wajen bikin kaddamar da kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar na kasa da na jihohi a hukumance.
Jihar Kogi ta APC ce daga tushe
Jaridar Guardian ta kara da cewa, tsohon gwamnan ya ce jihar Kogi ta APC ce daga tushe don haka, ya yi imanin cewa jama’a za su fito domin kada kuri’unsu ga jam’iyyar APC don jihar ta samu shugabanci nagari.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewarsa:
“Kun dandana kyakkyawan shugabanci daga gwamnatin Gwamna Yahaya Bello kuma a matsayinmu na jam’iyya muna fatan za mu kara yin aiki da mai rike da tutarmu, Alhaji Usman Ododo, da zarar an zabe shi.
“Ba mu sa ran samun nasarar kasa da 90% daga mutanen Kogi a zaben gwamnan da za a yi a ranar 11 ga watan Nuwamba.”
Shirin APC na kafa cibiyar nazarin siyasar ci gaba
A bangare guda, shugaban jam’iyyar APC mai mulki ta kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce jam’iyyar ta kammala shirye-shiryen bude ofisoshi na aiki a daukacin unguwanni 8,813 da ke fadin kasar nan, tare da kafa cibiyar nazari ta jam’iyyar.
Ganduje ya bayyana haka ne a ranar Asabar a yayin kaddamar da kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar na kasa na zaben gwamnan jihar Kogi da za a gudanar a ranar 11 ga watan Nuwamba, Daily Trust ta ruwaito.
Asali: Legit.ng