Jam’iyyar APC Za Ta Bude Cibiyar Nazarin Siyasar Ci Gaba Daidai Da Manufar Jam’iyya, Ganduje

Jam’iyyar APC Za Ta Bude Cibiyar Nazarin Siyasar Ci Gaba Daidai Da Manufar Jam’iyya, Ganduje

  • Shugaban APC na kasa ya bayyana shirin jam’iyyar na tabbatar da an kafa cibiyar nazarin ayyukan ci gaban dimokradiyya
  • Ya bayyana hakan ne a taron kaddamar da gangamin kamfen na jam’iyyar a shirin zaben da za a yi jihar Kogi nan ba da jimawa ba
  • Taron ya samu halartar jiga-jigai da dama, wadanda a halin yanzu suke rike da mukamai ko kuma suka kammala mulki

FCT, Abuja - Shugaban jam’iyyar APC mai mulki ta kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce jam’iyyar ta kammala shirye-shiryen bude ofisoshi na aiki a daukacin unguwanni 8,813 da ke fadin kasar nan, tare da kafa cibiyar nazari ta jam’iyyar.

Ganduje ya bayyana haka ne a ranar Asabar a yayin kaddamar da kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar na kasa na zaben gwamnan Jihar Kogi da za a gudanar a ranar 11 ga watan Nuwamba, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kaso 90% muke so: Ganduje ya gama shirin zaben jihar Arewa, ya fadi kuri'un da yake hari a APC

Ganduje ya fadi wasu abubuwa game da shirin APC
APC za ta bude cibiyar nazari | Hoto: Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Twitter

Jawabin tsohon gwamnan Kano Ganduje

Da yake jawabi a wurin taron, Ganduje ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Zan so in yi kira ga dukkan ‘yan jam’iyya da masu ruwa da tsaki da su hada karfi da karfe domin ganin jam’iyyar mu ta samu nasara.
“Ta yin haka, duk ayyukan da aka bari za su dore kuma za a ci gaba da gudanar da mulki. A matsayinmu na jam’iyya, mun himmatu wajen yin aiki tukuru domin cimma wadannan manufofi da tsaruka.
“Yana da kyau mu lura cewa mun fara kuma mun kammala tsare-tsare na tsara jam’iyyarmu ta zama jam’iyyar ci gaba ta gaskiya ta hanyar bude cikakkun ofisoshi a dukkan unguwanni 8,813 da ke Najeriya.”

Wadanda suka halarci taron

Daga nan ne ya bayyan manufar APC na kafa cibiyar karantar ilimin ci gaban dimokradiyya a kasar nan, kamar yadda rahoto ya bayyana.

Kara karanta wannan

Shugaban APC Na Ƙasa Ya Ɓullo da Sabon Tsari, Zai Gina Abu 1 a Kowace Gunduma a Najeriya

Gwamnonin jihohin Kogi, Ogun, Legas, Neja, Benue da Kwara sun halarci bikin kaddamarwar da dai sauran manyan jam’iyyar.

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da tsofaffin gwamnoni da sanatoci da sauran jiga-jigan jam’iyyar a fadin kasar nan.

Za mu kwace Rivers, inji Ganduje

A wani labarin, Shugaban jam’iyyar APC mai mulki ta kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya gargadi jam’iyyar PDP da ke shirin karbe jihar Rivers mai arzikin man fetur.

Ganduje ya yi wannan gargadin ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar gangamin Sanata Magnus Abe a ofishinsa da ke sakatariyar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja.

Da yake gargadin jam’iyya mai mulki a jihar kana bin da ke tafe, tsohon gwamnan na Kano ya ce da yarjejeniyar manyan tubalan APC guda uku a jihar nan ba da jimawa ba jam’iyyar mai mulki a jihar za ta tattara kwamutsanta zuwa wajen gidan gwamnati.

Kara karanta wannan

Karfin Hali: Ganduje Ya Hango Romo a Jihar PDP, Ya Ce Nan Kusa Zai Kwace Ya Ba APC

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.