'Yan KAROTA Sun Yi Babban Kamu, Sun Kame Jabun Magungunan da Kudinsu Ya Kai N5om a Jihar Kano
- Hukumar KAROTA a jihar Kano ta bayyana kame wasu magunguna da tace jabu ne daga wasu da suka shigo dasu Najeriya
- Ana yawan kame masu shigo da miyagun kwayoyi a Najeriya, musamman a jihohin da suke da habakar kasuwnaci irin Kano
- Jihar Kano na da jami’an KAROTA da ke kame da kuma kula zirganiyar ababen hawa a iyakoki da ma cikin binin Kano
Jihar Kano - KAROTA, hukumar da ke kula da zirga-zirgar ababen hawa a jihar Kano ta bayyana yadda jami’anta suka yi aikin kama wasu kawo jabun magunguna a jihar.
A cewar hukumar, an kama jabun magunguna da kudinsu ya kai Naira miliyan 50 a jihar da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.
Wannan na fitowa ne daga bakin mai magana da yawun hukumar Nabulisi Abubakar Kofar Na’isa a cikin wata sanarwar da ya fitar.
Yadda aka kama magungunan
Hukumar ya kuma bayyana cewa, an kama jabun magungunan ne a kan titin Murtala da ke birnin Kano, Aminiya ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar sanarwar:
“Lokacin da direban motar yake kokarin shiga kasuwar Sabon Gari domin rabawa masu shaguna.
“Daga cikin magungunan da aka cafke sun hada da: maganin ciwon jiki, maganin zazzabi, maganin tari da sauran su.”
Matsayar KAROTA kan mabarnata
Faisal Mahmud Kabir, shugaban KAROTA ya bayyana cewa, hukumar ba za ta duba ido a maida Kano matattarar miyagun kwayoyi ba.
Ya kuma gargadi jama’a da su guji sayen magungunan da ka iya jefa su a fitina ko wata babbar matsalar da za ta iya biyo ba na rashin lafiya ba.
Hakazalika, ya ce kofar hukumar a bude take a kowane lokaci domin jin ta bakin jama’a da kuma karbar shawari kan yaki da miyagun kwayoyi da jabun magunguna a jihar baki daya.
Za a takaita zirga-zirga
A wani labarin, gwamnatin jihar Kano ta janye wata dokar da ta sanya kan takaita zirga-zirgar baburan adaidaita sahu a kan wasu titunan jihar.
Baffa Abba Dan'agundi, shugaban hukumar KAROTA a jihar ne ya bayyana hakan a yau Laraba 30 ga watan Nuwamba.
Ya bayyana cewa, dakatarwar ta zama dole duba da yadda 'yan adaidaita sahu suka karbi dokar da aka saka, rahoton Platinum Post.
Asali: Legit.ng