Gwamnatin Najeriya Ta Magantu Kan Juyin Mulki Yayin Da Sojoji Suka Hambarar Da Gwamnati a Gabon Da Nijar
- Yayin da ake ci gaba da samun karuwar juyin mulki a nahiyar Afirka, gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi watsi da duk wata fargaba na juyin mulki
- A cewar gwamnatin tarayya, kasar ta wuci zamanin hambarar da gwamnati ta karfin tuwo
- Mohammed Idris Malagi, ministan labarai da wayar da kan yan kasa ya ce, Najeriya ta kasance kasar damokradiyya tsawon wannan lokaci inda cibiyoyin damokradiyya ke kara karfi
Abuja - Mohammed Idris, ministan labarai da wayar da kan yan kasa, ya yi watsi da fargabar da ake yi na kar sojoji su yi juyin mulki a Najeriya.
Idris ya ce kasar ta wuce wannan matakin da dadewa.
Juyin mulki: "Mun wuci wannan", minista
Ministan ya bayyana cewa cibiyoyin damokradiyya na da karfi sosai a Najeriya, don haka ba zai zama abu mai sauki ga manyan jami'an sojoji su hambarar da zababbun shugabannin damokradiyya ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
An bayyana matsayin gwamnatin tarayya ne a cikin wani rahoto da jaridar Punch ta fitar a ranar Asabar, 2 ga watan Agusta.
Ministan ya ce:
"Zan iya fara maku babu tsoro ko fargaba ko kadan. Mun wuci wannan, kuma mun kasance kasar damokradiyya tsawon wannan lokaci tare da cibiyoyin damokradiyya da ke kara karfi."
Juyin mulki: Fargabar da nake ta tabbata, Tinubu
A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa tsoron da ya dunga ji game da juyin mulkin sojoji a Jamhuriyar Nijar ya tabbata da abun da ya faru a Gabon inda sojoji suka tsige Shugaba Ali Bongo ta hanyar kifar da gwamnatinsa.
Shugaban kasar ya ce ya yi fargabar cewa matakin da sojojin juyin mulki a Jamhuriyar Nijar suka dauka zai kafa mummunan tarihi ga nahiyar bakar fata. Fadar shugaban kasa ta bayyana haka a cikin wata wallafa a manhajar X.
"Na ji dadin juyin mulkin Gabon" - Fayose
A wani labarin, mun ji cewa tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya nuna jin dadinsa dangane da juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar Gabon da ke Afrika ta tsakiya.
Fayose ya yi martani a kan hambarar da gwamnatin farar hula da sojojin suka yi a kasar Gabon a ranar Juma'a, 1 ga watan Satumba, rahoton Punch.
Asali: Legit.ng