Fitacciyar 'Yar Bautar Gargajiya, Iya Osun Ta Karbi Addinin Musulinci a Jihar Kwara

Fitacciyar 'Yar Bautar Gargajiya, Iya Osun Ta Karbi Addinin Musulinci a Jihar Kwara

  • Shahararriyar mai bin addinin gargajiyar nan a jihar Kwara, Iya Osun ta furta kalmar shahada, ta koma Musulunci
  • A wani Bidiyo da ke yawo, Iya Osun ta bayyana cewa ta karɓi addinin Musulunci ne bisa ra'ayin kanta, babu wanda ya tilasta mata
  • Iyalanta kama daga mahaifinta da 'ya'yanta sun nuna tsantsar farin cikinsu bisa wannan mataki da ta ɗauka

Kwara - Fitacciyar Malama a adddinin gargajiya a jihar Kwara, Abebi Ashabi Efunsetan Yakubu, ta koma Addinin Musulunci, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Duk da an haife ta a cikin Musulunci, ’yar gargajiya wacce aka fi sani da Iya Osun, daga yankin Ayegbami a Ilọrin, ta fita daga Musulunci kuma ta fito fili ta yi ikirarin addinin Isese (addinin gargajiya).

Iya Osun ta bar addinin gargajiya, ta koma Musulunci.
Fitacciyar 'Yar Bautar Gargajiya, Iya Osun Ta Karbi Addinin Musulinci a Jihar Kwara Hoto: Ibadan Cruise TV
Asali: Facebook

A wani faifan bidiyo da ke yawo, Iya Osun ta furta kalmar shahada wanda ke tabbatar da ta Musulunta kuma ta ce ta karɓi addinin Musulunci ne bisa ra'ayin kanta.

Kara karanta wannan

An Kama Malamin Addinin Musuluncin Da 'Yan Sanda Ke Nema Ruwa a Jallo a Jihar Arewa

A kalamanta, Iya Osun ta ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Ba bu wanda ya tilasta mun na karɓi Addinin Musulunci, amma na Musulunta ne domin na bi tafarkin Manzon Allah (SAW), Sahabbansa da kuma Malamai."
"Dama ban taɓa barin Addinin Musulunci gaba daya ba, amma ban san Allah kamar yadda nake zato ba har sai da ya bayyana kansa a rayuwata kuma na gane gaskiya."

Iyalanta sun yi farin ciki da ta Musulunta

Haka nan kuma, wani mutum da ya yi ikirarin cewa shi ne mahaifinta a cikin faifan bidiyon, ya gode wa Allah maɗaukakacin Sarki, wanda ya haskaka zuciyarta ta sake dawo wa Musulunci.

Ya ƙara da cewa wannan rana na ɗaya daga cikin ranakun da ba zai taɓa manta wa da su ba saboda farin cikin da yaji bayan shaida Musuluntar ɗiyarsa, Iya Osun.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamnatin Abba Gida-Gida Ta Fusata, Ta Kori Shugaban Fitaccen Asibiti Kan Muhimmin Abu

Ɗaya daga cikin 'ya'yanta, Abdulhakeem ya ce:

"Mahaifiyar mu ba ta bar Addinin Musulunci baki ɗaya ba, tana yin layya da Sallah, tana Azumin watan Ramadan kuma tana fitar da Zakkar fidda kai a duk ƙarshen Azumi."

Yan Sanda Sun Kama Malamin Musuluncin da Suke Nema Ruwa a Jallo

A wani rahoton na daban Jami'an rundunar 'yan sanda reshen jihar Kwara sun kama Malamin addinin Musuluncin nan da ake nema ruwa a jallo.

Rundunar tana neman malamin ne bisa zargin yi wa wasu 'yan addinin gargajiya barazana a Ilorin , babban birnin jihar Kwara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262