Tinubu Ya Sauya Wakilan Ondo da Cross River a Hukumar NDDC, Cikakken Bayani
- Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da gaggauta maye gurbin wakilin jihar Ondo a hukumar NDDC, Mista Victor Akinjo, da Hon Otito Atikase
- Chief Ajuri Ngelale, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin labarai ne ya bayyana hakan a ranar Juma'a, 1 ga watan Agusta
- Shugaban kasar ya kuma amince da gaggauta maye gurbin wakilin Cross River a NDDC, Mista Asi Oku Okang, da sabon wakili, Rt. Hon. Orok Otuk Duke
Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi gyare-gyare a nade-naden da ya yi a hukumar cigaban Neja Delta (NDDC) a ranar Juma'a, 1 ga watan Satumba.
Tinubu ya amince da sauya wakilan jihohin Ondo da Cross River a hukumar.
Wannan mataki na shugaban kasar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin labarai, Ajuri Ngelale ya fitar a yammacin ranar Juma'a, jaridar The Nation ta rahoto.
Tinubu ya kuma ce an sabonta nadin Dr Samuel Ogbuku inda zai ci gaba da aiki a matsayin mukadashin manajan darakta na hukumar har zuwa lokacin da majalisar dattawa za ta tabbatar da shi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sanarwar ta ce:
"Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da gaggauta maye gurbin wakilin jihar Ondo a hukumar NDDC, Mista Victor Akinjo, da sabon wakilin jihar Ondo, Hon. Otito Atikase.
"Shugaban kasar ya kuma amince da gaggauta maye gurbin wakilin jihar Cross River a hukumar NDDC, Mista Asi Oku Okang, da sabon wakilin jihar Cross River, Rt. Hon. Orok Otuk Duke.
"Bugu da kari, an sake nada manajan darakta/ shugaban NDDC, Dr. Samuel Ogbuku, a karo na biyu kuma zai ci gaba da aiki a matsayin mukaddashin hukumar, har zuwa lokacin da majalisar dattawa za ta tabbatar da sake nadin nasa."
Tinubu ya nada sabbin shugabannin gudanarwa na hukumar NDDC
A gefe guda, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin sabon kwamitin gudanarwa na hukumar raya yankin Neja Delta (NDDC).
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale, ya fitar a daren ranar Talata kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Asali: Legit.ng