Dubun Dan Daba Da Ake Nema Ruwa A Jallo Ta Cika A Kano Bayan 'Yan Sanda Sun Cafke Shi
- Dubun dan daba da ake nema ruwa a jallo ta cika a yau Juma'a bayan jami'an tsaro sun damke shi a Kano
- Wanda ake zargin, Sadiq Ahmad da aka fi sani da 'Big Star' ya shiga hannu bayan ji wa wani dattijo rauni da almakashi
- 'Big Star' na daga cikin 'yan daba da ake nema ruwa a jallo inda wasu daga cikinsu su ka mika wuya tare da tuba daga aikata laifuka
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kano - Rundunar 'yan sanda a jihar Kano sun cafke wani dan daba da ake nema ruwa a jallo.
Wanda aka kaman mai suna Sadiq Ahmad da aka fi sani da 'Big Star' ya shiga hannu bayan illata wani da makami.
Wasu 'yan daba ake nema a Kano ruwa a jallo?
Sadiq mai shekaru 33 na daga cikin 'yan daba da ake nema ruwa a jallo a jihar bayan wasu sun mika wuya tare da tuba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kakakin rundunar a jihar, Abdullahi Kiyawa shi ya bayyana haka a yau Juma'a 1 ga watan Satumba a Kano cewar Tori News.
Kiyawa ya ce dan daban ya na bangaren binciken laifuka na hukumar inda su ke gudanar da binciken sirri.
Meye 'yan sandan su ka ce kan 'yan daba a Kano?
Sanarwar ta ce:
"A kokarin rundunar 'yan sanda na farautar 'yan daba a jihar wadanda ake nema ruwa a jallo.
"An yi nasarar kama Sadiq Ahmad da aka fi sani da 'Big Star' mai shekaru 33 a unguwar Dorayi karama da ke Kano.
"Sadiq ya shiga hannu bayan kama shi da almakashi tare da ji wa wani Abdulrahman Isah mai shekaru 50 rauni"
PM News ta tattaro cewa an dauki dattijon zuwa asibitin Murtala tare da masa magani yayin da aka sallame shi.
Yayin martanin shi, Sadiq ya ce:
"A baya ina amfani da kwayoyi kamar wiwi da sauran kayan maye na kwalabe yayin da nake aikata laifukan."
Kano: Kasurgumin Dan Daba Da 'Yan Sanda Ke Nema Ruwa A Jallo Ya Mika Wuya
A wani labarin, Kasurgumin dan daba da ‘yan sanda ke nema ruwa a jallo a Kano mai suna Nasiru Abdullahi da aka fi sani da Chile Mai Doki ya mika wuya ga hukumar.
A makon da ya gabata ne rundunar 'yan sanda a jihar ta sanar da sunayen ‘yan daba uku da take nema ruwa a jallo tare da ba da kyautar N300,000 ga duk wanda ya kawo su.
Asali: Legit.ng