Murna Yayin Da Gwamnatin Najeriya Ta Sanar Da Ranar Biyan Basusukan Masu N-Power
- Gwamnatin Tarayya ta ce a shirye ta ke ta fara biyan basusukan da wadanda ke shirin N-Power ke bin ta
- Masu kula da shirin na N-Power ne suka sanar da hakan yayin taro da wasu masu amfana da shirin a taron a Abuja
- Legit.ng ta rahoto cewa an kirkiri shirin na N-Power a ranar 8 ga watan Yunin 2016, karkashin gwamnatin jam'iyyar All Progressives Congress, APC, domin magnce matsalar karancin ayyukan yi da kuma inganta walwala da cigaba
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayyar Najeriya a ranar Litinin, 16 ga watan Oktoba, ta ce za ta fara biyan bashin alawus dinsu na watanni 9 a Nuwamban 2023.
Manajan shirin N-Power na kasa, Akindele Egbuwalo ne ya bayyana hakan a cewar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Allawus: Za a biya bashin da masu N-Power ke bi
Wannan sabon bayanin na kunshe cikin sanarwar da jami'in watsa labarai na shirin National Social Investment Program Agency (NSIPA), Jamaluddeen Kabir ya fitar ne. Wani rahoto na Vanguard shine ya tabbatar da sanarwar ta NSIPA.
Wani sashi na jawabin na NSIPA ya ce:
"Sakamakon dakatar da shirin na dan wani lokaci saboda garambawul da binciken kwa-kwaf, an gano wasu kudade daga masu kula da shirin kuma an yi shirin fara biyan basuka da watanni 9 daga Nuwamban 2023.
"Za a biya kudaden ne daki-daki."
Legit Hausa ta rahoto cewa masu amfana da shirin na N-Power daga bangaren ilimi, lafiya da aikin noma duk suna karbar N30,000 ne duk wata.
Dakaci karin bayani ...
Asali: Legit.ng