Cire Tallafi: Gwamnatin Gombe Ta Amince Da Ƙara Wa Ma'aikata Albashi Da N10,000

Cire Tallafi: Gwamnatin Gombe Ta Amince Da Ƙara Wa Ma'aikata Albashi Da N10,000

  • Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya amince da ƙara wa ma'aikata albashi da N10,000
  • Ya ce ƙarin zai fara aiki daga watan Agusta kuma an yi shi ne domin rage musu zafin matsin tattalin arzikin da aka shiga bayan cire tallafin man fetur
  • Wannan na ɗaya daga cikin matakan da gwamnatin Gombe ta ɗauka domin inganta walwalar ma'aikatanta

Gombe - Gwamnatin jihar Gombe karƙashin jagorancin gwamna Muhammad Inuwa Yahaya, ta amince da ƙara wa ma'aikatan jihar albashi.

Gwamnatin ta amince da ƙara wa kowane ma'aikaci a kowane mataki N10,000 a albashinsa domin rage wahalhalun cire tallafin man fetur, The Nation ta rahoto.

Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya.
Cire Tallafi: Gwamnatin Gombe Ta Amince Da Ƙara Wa Ma'aikata Albashi Da N10,000 Hoto: Muhammad Inuwa Yahaya
Asali: Facebook

Mataimakin gwamnan jihar Gombe, Manassah Daniel Jatau, shi ne ya bayyana wannan tagomashi yayin zantawa da manema labarai a Gombe ranar Jumu'a.

Ya ce ƙarin albashin ɗaya ne daga cikin matakan da gwamna Inuwa Yahaya ya ɗauka domin rage wahalar matsin tattalin arzikin da jama'a suka shiga bayan cire tallafin.

Kara karanta wannan

An Bayyana Babban Abu 1 Da Ya Jawo Ƙaruwar Juyin Mulkin Sojoji a Nahiyar Afirka

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce Gwamna Inuwa Yahaya ya damu matuƙa da walwala da jin dadin ma’aikata da mazauna jihar ta hanyar bada tallafi daban-daban tun bayan barkewar cutar ta COVID-19.

Mataimakin gwamnan ya ce tun bayan cire tallafin man fetur, gwamnatin jihar ta dauki matakin rage illa da ƙuncin da lamarin ya jefa al'ummar jihar.

A cewarsa, ɗaya cikin matakan da gwamnati ta ɗauka kawo yanzu shi ne raba kayayyaki ga mutane 30,000, kuma a tsarin, aƙalla mutane 420,000 zasu ci gajiya a Gombe.

Yaushe gwamnatin zata aiwatar da ƙarin albashin?

A cewarsa, ƙarin N10,000 zai shafi ma’aikatan jiha da na kananan hukumomi, kuma zai fara aiki daga watan Agusta, 2023, kamar yadda Dailypost ta rahoto.

Daniel Jatau ya ce:

“Mun lura da irin matsalolin da ma’aikata ke fuskanta sakamakon tabarbarewar tattalin arziki, don haka muka yanke shawarar agaza musu da Naira 10,000 kowane wata, wanda zai fara daga watan Agusta, 2023."

Kara karanta wannan

"Za a Ji Daɗi" Babban Abinda Shugaba Tinubu Ya Yi da Kuɗin Tallafin Fetur Ya Bayyana

Yayin da aka tambaye shi tsawon lokacin da gwamnati zata shafe tana biyan kowane ma'aikaci wannan ƙarin na N10,000, ya ce, "Ba a ƙayyade lokaci ba a yanzu."

Iyorchia Ayu Zai Koma Matsayinsa Na Shugaban PDP Na Ƙasa? Kotu Ta Yanke Hukunci

A wani rahoton na daban Babbar kotun jihar Benuwai mai zama a Gboko ta yanke hukunci kan ƙarar da ta nemi a maida Iyorchia Ayu a matsayin shugaban PDP.

Alkalin Kotun, mai shari'a D. M Igyuse, ya kori ƙarar, inda ya bayyana ta da cin mutuncin matakan shari'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262