Wani Matashi Ya Buga Wa Budurwarsa Guduma Har Lahira Saboda Gudun Yaudara
- 'Yan sanda sun cafke wani matashi da ake zargin ya buga wa budurwarsa guduma har lahira saboda gudun yaudara
- Kwamishinan 'yan sanda jihar Legas, Idowu Owohunwa, ya ce wanda ake zargin ya ce ya ga alamun zata rabu da shi shiyasa ya kashe ta
- Ya kuma kara da cewa a cikin wata ɗaya, dakarun yan sanda sun kama masu aikata muggan laifuka da dama
Jihar Legas - Hukumar 'yan sanda reshen jIhar Legas ta bayyana cewa jami'anta sun cafke wani matashi, Samuel Adeniyi, bisa zargin halaka budurwarsa da guduma.
Hukumar 'yan sandan ta ce matashin ya halaka budurwarsa ne ta hanyar buga mata guduma a kai a wata Anguwa da har yanzu ba a bayyana ba a jihar Legas.
Kwamishinan 'yan sandan jihar, Idowu Owohunwa, shi ne ya bayyana haka yayin zantawa da 'yan jarida a babban ofishin 'yan sanda dake Ikeja ranar Alhamis, Punch ta ruwaito.
Owohunwa ya ce dalilin da ya sa saurayinya kashe budurwarsa shi ne saboda ya damu cewa zata iya guje masa ta koma wurin wani mutum daban, rahoton The Angle ya tabbatar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Da yake nuna wanda ake zargin, kwamishinan 'yan sandan ya ce:
"Kishi ya ɗebi wani matashi mai suna Samuel Adeniyi inda ya farfasa kan budurwarsa har ta mutu. Ya ce yana zargin tana shirin yaudararsa ta koma wurin wani, bisa haka ya halaka ta kuma ya gudu."
"Mun samu nasarar damƙe shi kuma mun kwato gudumar da ya yi amfani da ita wajen aikata kisan, nan ba da jimawa ba zamu gurfanar da shi a gaban Kotu."
'Yan sanda sun samu nasarori a Legas
Bugu da ƙari, kwamishinan 'yan sandan ya bayyana cewa cikin wata ɗaya da kaddamar da Operation Flush, jami'an 'yan sanda sun samu gagarumar nasara.
Ya ce a tsawon wannan lokacin, dakaraun 'yan sanda sun kai samame maɓoyar masu aikata muggan laifuka da yawa, inda suka kama 'yan ƙungiyoyin asiri, 'yan fashi da sauransu.
Yan Bindiga Sun Fara Amfani Da Dabarun 'Yan Ta'adda Don Yin Barna, Sojoji
A wani rahoton kuma Rundunar soji ta bayyana wasu dabaru da 'yan bindiga suka fara ɓullo wa da su a arewacin Najeriya.
Babban hafsan rundunar sojin ƙasa, Janar Taoreed Abiodun Lagbaja, ya ce sojoji ba zasu yi ƙasa a guiwa ba wajen murkushe yan ta'adda.
Asali: Legit.ng