Jiragen Sojoji Guda Biyu Sun Yi Hatsari, Dakaru 6 Sun Riga Mu Gidan Gaskiya

Jiragen Sojoji Guda Biyu Sun Yi Hatsari, Dakaru 6 Sun Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Jami'an soji 6 sun kwanta dama yayin da wasu jiragen sojoji masu saukar ungulu suka yi hatsari ranar Alhamis
  • Bayanai sun nuna cewa jiragen sun faɗo ne yayin da suke atisayen yaƙi a gabashin ƙasar Ukraine
  • Har yanzun babu cikakken bayani kan abinda ya haddasa hatsarin amma SBI ta ce za a gudanar da bincike mai zurfi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Ukraine - Jami'an sojojin ƙasar Ukraine guda 6 sun rasa rayukansu yayin da wasu jirage masu saukar ungulu guda biyu mallakin rundunar sojin ƙasar suka gamu da hatsari.

Channels tv ta tattaro cewa wasu masu bincike a ƙasar Ukraine sun bayyana cewa jiragen Helikwafta na sojojin sun faɗo ne yayin da suke wani Atisaye a gabashin ƙasar.

Jami'an sojin ƙasar Ukraine.
Jiragen Sojoji Guda Biyu Sun Yi Hatsari, Dakaru 6 Sun Riga Mu Gidan Gaskiya Hoto: Channels
Asali: UGC

Bayanai sun nuna cewa mummunan hatsarin jiragen ya auku ne ranar Alhamis a yankin Kramatorsk da ke gabashin Donetsk.

Kara karanta wannan

Bayan Juyin Mulkin Gabon, Shugaba Tinubu Ya Faɗi Ainihin Abinda Yake Jin Tsoron Ya Faru

Hukumar bincike ta ƙasar Ukraine (SBI) ba ta yi cikakken bayani kan abinda ya faru ba har kawo yanzu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Jiragen sama masu saukar ungulu na Mi-8 guda biyu sun yi hatsari a yayin wani atisayen yaki. Jami’an Sojin kasar Ukraine guda shida sun mutu,” in ji SBI a wata sanarwa da ta fitar.

Yadda za a gudanar da bincike kan hatsarin

Ta ƙara da cewa hukumar tattara bayanan sirri, a bincikenta zata maida hankali kan yiwuwar saɓa dokar tsaro yayin shirye-shiryen tashin jiragen, wanda babban laifi ne a doka.

Binciken zai kuma duba "yiwuwar zagon kasa ko kuma harbo jiragen biyu masu saukar ungulu daga maƙiya", in ji SBI.

Ta ce masu binciken za su binciki bayanai daga na'urar rikodin ta jiragen tare da duba yanayin fasahar jiragen helikwafta, Aljazeera ta rahoto.

Kara karanta wannan

An Bayyana Babban Abu 1 Da Ya Jawo Ƙaruwar Juyin Mulkin Sojoji a Nahiyar Afirka

Ukraine na amfani da jirage masu saukar ungulu na soja na Mi-8 a fagen fama, duk da cewa jirgin wanda Tarayyar Soviet ta kera ana amfani da shi ne wajen safuri. Kowane helikwafta yana da ma'aikata uku.

Yawancin jiragen helikwafta ƙirar Mi-8 da Ukraine ke amfani da su sun tsufa, amma ta samu gudummawar ƙarin jirage na zamani daga ƙawayenta.

Talauci Ne Babban Abinda Ke Haddasa Juyin Mulki a Nahiyar Afirka, Falana

A wani rahoton kuma babban lauyan nan ɗan gwagwarmayar kare haƙƙin Bil'Adama, Femi Falana, ya bayyana babban abinda ke haddasa juyin mulki a Afirka.

Lauyan ya bayyana cewa yawan talauci ne ke jawo ƙaruwar juyin mulkin da sojoji ke yi a nahiyar Afirka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262