Matsalar Tsaro: Har Yanzun Akwai Yan Najeriya Sama da 23,000 da Suka Ɓata, FG
- Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa har yanzun akwai adadin mutane aƙalla 23,000 da suka ɓata a faɗin ƙasar nan
- Ministar harkokin jin ƙai da yaƙi da talauci, Betta Edu, ta ce mutanen sun ɓace ne sakamakon matsalolin tsaro
- A cewarta, har yanzun gwamnati bata san ainihin yawan mutanen da suka ɓace ba ta hanyar garkuwa, yan bindiga da sauransu
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT Abuja - Gwamnatin tarayyan Najeriya ta tabbatar da cewa har yanzun akwai mutane aƙalla 23,000 da ba a san inda suke ba sakamakon taɓarɓarewar tsaro a ƙasa.
Gwamnatin ta ce mutanen, waɗanda aka nema aka rasa ta yanayi daban-daban kama daga ayyukan yan bindiga, garkuwa da mutane da sauransu, har yau ba a gansu ba.
Ministar jin ƙai da yaye talauci, Dakta Betta Edu ce ta bayyana haka a wurin taron ranar mutanen da suka ɓace wanda ya gudana a hukumar kare haƙƙin ɗan adam da ke Abuja.
Misis Edu ta ƙara da bayanin cewa har yanzun gwamnati ba ta san taƙamaiman adadin yawan mutanen da suka ɓace ba a faɗin ƙasar nan, Daily Trust ta rahoto.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wane shiri FG zata yi don gano mutanen?
Edu, wacce Daraktan sashin ayyuka jin ƙai, Ali Grema, ya wakilta a wurin taron, ta ce ana bukatar ingantacciyar hanya don inganta bayar da rahoto da kuma gano mutanen da suka bata.
Vanguard ta ruwaito Betta Edu na cewa:
“A Najeriya, rahoto ya nuna cewa cikin kasa da shekaru goma, sama da mutane 25,000 ne aka kai ƙorafin sun ɓata ga ICRC da kungiyar agaji ta Red Cross sakamakon tashe tashen hankula a yankin Arewa maso Gabas."
"Wannan adadi ya kai rabin mutanen da suka ɓata a faɗin Afirka. Har yau ba a san inda mutane sama da 23,000 suka shiga ba. Alamu sun nuna dole a inganta matakan tattara rahoto don gano waɗanda suka ɓata."
Har yanzu ba a tantance ainihin adadin mutanen da suka bace a kasar nan ba."
Shugaba Tinubu Ya Dakatar Da Wasu Manyan Ayyuka 2 Da Buhari Ya Fara
A wani labarin na daban kuma Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya bada umurnin dakatar da sallama filin tashin jiragen sama da kamfanin jirgin sama na kasa.
Idan za a iya tunawa an amince da yin ayyukan ne a kusan karshen wa'adin gwamnatin Shugaba Buhari , kuma hakan ya janyo cece-kuce.
Asali: Legit.ng